"Bai So": Buba Galadima Ya Fadi Dalilin Jawo Buhari cikin Harkar Siyasa

"Bai So": Buba Galadima Ya Fadi Dalilin Jawo Buhari cikin Harkar Siyasa

  • Babban ƙusa a jan'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya taɓo tarihin fara siyasar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Buba Galadima ya bayyana cewa Buhari bai da ra'ayin siyasa saboda yana kallon masu yin ta a matsayin marasa gaskiya
  • Ya ce su ne suka jawo Buharo cikin siyasa domin cimma wata manufa da suke da ita kan gwamnatin Olusegun Obasanjo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana dalilin da ya sa suka jawo Muhammadu Buhari cikin siyasa.

Buba Galadima ya bayyana cewa wata ƙungiya daga Arewacin Najeriya ce ta shigo da Muhammadu Buhari cikin siyasa domin tinkarar ayyukan ƙungiyar Oduduwa Peoples Congress (OPC).

Buba Galadima ya yi magana kan Buhari
Buba Galadima ya ce su suka jawo Buhari cikin siyasa Hoto: Buba Galadima, Muhammadu Buhari
Source: UGC

Buba Galadima ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Morning Show na tashar Arise Tv.

Kara karanta wannan

Shekarau ya yi alhinin rasuwar Buhari, ya bayyana wani halinsa da ya sani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Tribune ta ce OPC ta mamaye garin Ilorin a shekarun 1999 da 2000, da nufin rushe tsarin da Fulani ke da shi a yankin, abin da ƙungiyar daga Arewa ta ɗauka a matsayin barazana da wuce gona da iri.

Saboda rashin gamsuwa da yadda tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da gwamnan jihar Legas na lokacin, Bola Tinubu, ke kallon al’amarin ba tare da ɗaukar mataki ba, Buba Galadima da wasu mutum 33 suka taru a Kaduna domin samo mafita.

Buba Galadima ya ce ƙungiyar daga Arewa ta yanke shawarar marawa Buhari, tsohon soja, baya a siyasa domin ya tunkari barazanar OPC.

Meyasa aka jawo Buhari cikin siyasa?

Ya ƙara da cewa Buhari bai da sha’awar siyasa tun farko, domin yana ganin ƴan siyasa ba su da gaskiya.

Sai dai bayan ƙarfafa masa gwiwa da lallashi daga ɓangaren ƙungiyar, ya amince da shiga harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Buhari: Diyar tsohon shugaban kasa ta fadi halin da ta shiga bayan rasuwar mahaifinta

Bayan ya shiga siyasa, an daƙile ayyukan OPC, kuma gwamnatin Obasanjo ta ɗauki matakan hana ƙungiyar ci gaba da irin ayyukanta.

“Daga cikinmu da muka shigo da Buhari cikin siyasa mun yi hakan ne da wata manufa. Kuma yau zan bayyana wannan manufa."
"Janar Buhari bai fito daga fagen siyasa ba. Bai taɓa son siyasa ba saboda yana ganin ƴan siyasa ba su da gaskiya."
"Amma wani lamari ne ya sa muka yanke shawarar shigo da shi, muka lallashe shi, har wasu daga cikinmu suka tuntuɓe shi don shigo da shi siyasa, duk da muna da ajandar mu daban."
“A shekarar 1999 da 2000, OPC ta addabi wasu yankuna na ƙasar nan, musamman a Kudu maso Yamma, har ta hana mutane da dama zaman lafiya. Har suka tara motoci fiye da 500 domin mamaye Ilorin da nufin rusa tsarin Fulani a can."
“Mun ga wannan abin yayi yawa, kuma Shugaba Obasanjo bai yi komai ba. Bola Tinubu, wanda ke gwamnan Legas a lokacin, shima bai dauki mataki ba."
"Mun kuma ji kamar waɗannan ƙungiyoyin na samun ƙwarin gwiwa daga shugabanninsu da ke madafun iko. To me za mu yi?

Kara karanta wannan

Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya ta yi wa Buhari shaida mai kyau

“Na kira taro a Kaduna, mu kusan mutum 34, muka zauna muka fara tunani. Ta yaya za mu ceci mutanenmu daga wannan barazana ta OPC?"
“Na bayar da shawarar cewa akwai hanyoyi biyu ne kacal da ake kawar da gwamnati, ta hanyar bindiga ko kuma ta akwatin zaɓe. Wasu suka ce ba zai yiwu a ƙalubalanci Obasanjo ba. Sai muka tuno da Buhari."
“Lokacin da muka tunkare shi, bai ce zai shiga ba, amma kalamansa kan ƴan siyasa sun yi zafi. Duk da haka, tunda bai ce ba zai shiga ba, sai muka ci gaba da lallaɓarsa."
“A takaice, mun cimma manufarmu ta farko wato hana OPC ci gaba da irin waɗannan ayyuka. Buhari na shiga siyasa, sai muka shirya wani babban taro na ƙaddamar da shi cikin harkokinta."
"Gwamnatin Obasanjo ta firgita matuka. Sai ta fara ɗaukar matakan daƙile OPC a hukumance."
“Don haka, mun cimma manufarmu ta farko na shigo da Janar Buhari cikin siyasa. Sauran kuma ya zama tarihi."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya yi magana kan Buhari
Buba Galadima ya bayyana dalilin shigo da Buhari siyasa Hoto: Buba Galadima
Source: Facebook

Shekarau ya yi ta'aziyyar Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya yi ta'aziyyar Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

An fadi lokacin da ake sa ran birne Muhammadu Buhari a Daura

Shekarau ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya wamda ya yi bankwana da duniya a ranar Lahadi.

Tsohon gwamnan ya bayyana Buhari a matsayin mutum wanda yake ƙaunar Najeriya da al'ummarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng