Fadar Shugaban Kasa Ta Caccaki El Rufai, Ta Fadi Abin da Zai Sa Tinubu Ya Yi Tazarce a 2027

Fadar Shugaban Kasa Ta Caccaki El Rufai, Ta Fadi Abin da Zai Sa Tinubu Ya Yi Tazarce a 2027

  • Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya yi martani ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
  • Sunday Dare ya bayyana cewa El-Rufai bai da wani tasiri a harkar zaɓe da zai hana Shugaba Bola Tinubu samun tazarce
  • Hadimin shugaban ƙasan ya nuna cewa Bola Tinubu zai samu tazarce a babban zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa na jama'a, Sunday Dare, ya yi wa Nasir El-Rufai martani.

Tsohon ministan wasannin ya ce Nasir El-Rufai ba shi da wani ƙarin tasiri a harkar zaɓe fiye da kowanne ɗan Najeriya.

Sunday Dare ya caccaki El-Rufai kan Tinubu
Sunday Dare ya yi wa El-Rufai martani kan Tinubu Hoto: @elrufai, @DOlusegun
Source: Twitter

Sunday Dare ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Mic On Podcast wanda aka watsa a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Garba Shehu ya fadi halin da Buhari yake ciki bayan kwantar da shi a asibitin Landan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya-bayan nan, El-Rufai ya bayyana cewa haɗakar jam’iyyun adawa zai mayar da Shugaba Bola Tinubu Legas a zaɓen 2027.

Hadimin Tinubu ya yi wa El-Rufai martani

Sai dai, a yayin hirar Sunday Dare ya ce sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya kawo za su tabbatar da nasararsa a wa’adin mulki na biyu.

"Shin El-Rufai ne mutanen da suka kai miliyan 110 da za su kaɗa ƙuri’a? Nawa ne adadin masu kaɗa ƙuri’a da El-Rufai ke da su? Ko da yana da su, shin zai iya tilasta musu su zabi wanda ya ke so?"
"Ina girmama El-Rufai, amma wannan tunanin da ake da shi cewa El-Rufai tamkar Najeriya ne da miliyoyin ƙuri’u, hakan ya yi yawa sosai."

- Sunday Dare

Ya ƙara da cewa akwai ƴan siyasa da ke da ƙarin rinjaye, tasiri, da muhimmanci wajen sauya fasalin Najeriya.

“El-Rufai bai fi kowanne ɗan Najeriya ba, domin kowa na da haƙƙi a cikin ƙasar nan."

Kara karanta wannan

El Rufai ya ajiye adawa, ya yi nasiha ga mutanen gwamnatin Tinubu

- Sunday Dare

Sunday Dare ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasara a zaɓen 2027, musamman saboda manufofi da sauye-sauyen da ya samar.

'Tinubu na gyara Najeriya' - Sunday Dare

Sunday Dare ya bayyana cewa masana sun yi hasashen cewa ƴan Najeriya za su fara jin tasirin sauye-sauyen Shugaba Tinubu tsakanin shekaru huɗu zuwa shida.

Sunday Dare ya kare Shugaba Tinubu
Sunday Dare ya yi wa.El-Rufai.martani kan Tinubu Hoto: @SundayDareSD, @DOlusegun
Source: Twitter
"Idan ka kalli daidaiton manufofin gwamnati da ke taɓa manyan fannoni na tattalin arziƙi, kamar ma’adanan ƙasa, musamman lithium da tagulla, shugaban ƙasa ya mayar da hankali sosai kan wannan fanni."
"A ɓangaren man fetur, labarin da ake da shi a baya ya sha bamban da na yanzu. Haka kuma, akwai ci gaba a fannonin ilimi, noma da lafiya."
"A halin yanzu, cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 5,000 ana sabunta su, kuma tuni 1,000 daga ciki sun fara aiki gaba ɗaya."

- Sunday Dare

Malami ya gargaɗi Tinubu kan 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya aika da saƙon gargaɗi ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke tsakanin mutanen Tinubu da Buhari, an fara musayar yawu kan zaben 2015

Primate Ayodele ya buƙaci Tinubu da ya yi taka tsan-tsan da gwamnonin da suke komawa jam'iyyar APC domin za su ba shi matsala a zaɓen 2027.

Hakazalika ya shawarce shi kan ya yi hankali da wasu daga cikin masu muƙami a gwamnatinsa domin maƙiyansa ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng