2027: ADC Ta Samu Karuwa, Sanatar LP Ta Koma Tafiyarsu Atiku
- Jam'iyyar LP mai adawa a Najeriya ta rasa ɗaya daga cikin sanatocin da take da su a majalisar dattawa
- Sanata Ireti Kingibe mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja ta sanar da ficewarta daga LP zuwa jam'iyyar ADC
- Ireti Kingibe ta bayyana cewa za ta shirya shagali na musamman domin a yi murnar komawarta ADC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Abuja a majalisar dattawa, Sanata Ireti Kingibe, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar LP.
Sanata Ireti Kingibe ta kuma koma zuwa jam’iyyar ADC gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce Sanata Ireti Kingibe ta bayyana hakan ne yayin da take magana da manema labarai a Abuja.
Sanata Ireti Kingibe ta koma ADC
Ireti Kingibe ta ce ta sauya jam’iyyar ne bisa ƙashin kanta, kuma za a yi murnar hakan cikin shagali da ƙayatarwa.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya sun fara nuna wanda suke so jam'iyyar haɗaka ADC ta tsayar takara a 2027
"Na sadaukar da kaina gaba ɗaya ga jam’iyyar ADC."
"Amma fa, a matsayin sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja, kada ku zata zan tafi na yanki katin jam’iyya tamkar na tafi hutu. Ina son na yi hakan ne cikin hayaniya da shagali."
- Sanata Ireti Kingibe
Da aka tambaye ta ko tana da gamsuwa da jagorancin ADC da haɗakar siyasar da ta shiga, sanatar ta ce jam’iyyar har yanzu tana kan ci gaba da haɓaka, rahoton Vanguard ya tabbatar.
“Abu ne da ke kan hanyar haɓaka. Saboda haka ba za ka iya cewa yayin da ɗanka ke rarrafe ba, ba ka ji daɗin yadda zai iya gudu ba. Ka jira. Muna girma."
- Sanata Ireti Kingibe
Meyasa Ireti ta fice daga LP?
Dangane da damuwar da wasu ke da ita cewa sauya sheƙarta na iya sa ta rasa kujerar sanata bisa tanadin kundin tsarin mulki, Kingibe ta ce jam’iyyar LP a halin yanzu ta kasu gida biyu inda ta ce hakan ya ba ta damar sauya jam’iyya bisa doka.

Kara karanta wannan
ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

Source: Twitter
“Ina roƙonku da ku karanta kundin tsarin mulki. Akwai ɓangarori biyu na jam’iyyar LP a fili. Wannan ne cikakken ma’anar da kundin tsarin mulki ya bayar wadda ke ba mutum damar sauya jam’iyya ba tare da hukunci ba."
“To ku ce zauna a LP, to a wane ɓangare na jam’iyyar kuke so na zauna?
“Amma ni ina bin doka. Kuma da babu ɓangarori biyu na LP a fili, da ba zan taɓa tunanin sauya jam’iyya ba, saboda hakan ba ya bisa doka. Amma a halin yanzu akwai."
- Sanata Ireti Kingibe
Sanata Ireti Kingibe ta takali Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja, Ireti Kingibe ta caccaki ministan babban birnin tarayya Abuja.
Sanata Ireti Kingibe ta bayyana cewa talakawan Abuja ba su amfana da ayyukan da Wike yake yi a Abuja.
Ta bayyana cewa tsohon ministan Abuja, Nasir Ahmad El-Rufai ya fi Wike yin aiki mai amfani lokacin da ya hau kan kujerar.
Asali: Legit.ng
