An Zargi Kwankwaso da Jawo Rashin Shigar NNPP zaben Legas

An Zargi Kwankwaso da Jawo Rashin Shigar NNPP zaben Legas

  • Jam’iyyar NNPP ta ce rikicin cikin gida da jinkirin INEC sun hana ta tsayawa takarar kujerun kananan hukumomi a Lagos
  • Kwamitin zartarwa na kasa ya zargi bangaren Rabiu Kwankwaso da yunkurin karbe shugabanci ba bisa ka’ida ba
  • Duk da ikirarin kan nasarorin da suka samu a kotu, tsagin jam’iyyar ya ce bai samu damar gudanar da kamfen da cike ‘yan takara ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa ba ta shiga zaben kananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar Lagos ba.

Tsagin jam'iyyar da ke adawa da Rabiu Musa Kwankwaso ya ce hakan ta faru ne saboda matsalolin cikin gida da kuma jinkirin da hukumar INEC ta yi wajen sabunta bayananta.

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani kan maganar yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Tsagin NNPP ya zargi Kwankwaso kan gaza shiga zaben Legas
Tsagin NNPP ya zargi Kwankwaso kan gaza shiga zaben Legas. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa jami’in yada labarai na kasa na NNPP, Ogini Olaposi, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Lagos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogini Olaposi ya bayyana cewa rikicin shugabanci tsakanin bangaren Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da na Agbo Major ya hana jam’iyyar tsayawa takara.

Rikicin cikin gida ya hana NNPP takara

Olaposi ya ce rikicin da ya kunno kai bayan yunkurin Kwankwaso na karbe shugabancin jam’iyyar ya dauke hankalin jam’iyyar daga shiri da cike ‘yan takara.

A cewarsa:

“Tun kafin zaben, mun kasance cikin rikicin cikin gida bayan yunkurin bangaren Kwankwaso na karbe shugabancin jam’iyya.
"Wannan rikici ya hana mu gudanar da shirye-shiryen zabe yadda ya kamata.”

Ya kara da cewa ko da yake kotu ta yanke hukunci sau biyu a tana ba su nasara, hakan bai isar da su shawo kan matsalolin cikin gida ba.

Jinkirin INEC ya kara dagula NNPP a Legas

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

Olaposi ya zargi hukumar zabe ta kasa (INEC) da jinkiri wajen sabunta bayanan jam’iyyar a shafin ta, wanda ya hana kwamitin Agbo Major samun sahihancin da zai ba su damar shiga zaben.

Vanguard ta wallafa cewa Olaposi ya ce:

“INEC ba ta sabunta bayananmu ba a kan lokaci, hakan ya kara dagula al’amura saboda ba a tantance sabon kwamitin mu na kasa yadda ya kamata ba,”

Legas: 'Yan NNPP za su zabi wata jam'iyya

Bayan taron gaggawa da kwamitin zartarwa na kasa (NEC) ya gudanar a Abuja, Olaposi ya ce sun dauki mataki kan zaben.

Ya ce an umurci shugabar jam’iyyar NNPP ta jihar Lagos, Hajiya Anikè Adebowale, da ta ja ragamar tabbatar da mambobi sun goyi bayan wata jam’iyya da ra’ayinta ya yi daidai da na NNPP.

Olaposi ya ce duk da kalubalen da suka fuskanta a wannan lokaci, NNPP za ta ci gaba da tafiya da akidarta ta siyasa domin gyara Najeriya ta hanyar dimokuradiyya.

NNPP za ta zabi wata jam'iyya a zaben Legas
NNPP za ta zabi wata jam'iyya a zaben Legas. Hoto: INEC Nigeria
Source: Getty Images

Kwankwaso ya hadu da 'yan siyasa a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da 'yan siyasa da dama a Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan zargin badakala, Peter Obi ya fadi alakar da ta hada shi da Abacha

Hakan na zuwa ne bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu da su ne yayin kaddamar da wani littafi a Abuja.

Tsohon ministan shari'a a lokacin Goodluck Jonathan, Mohammed Bello Adoke ne ya wallafa littafi kan badakalar Malabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng