An Jiyo Abin da Tinubu Ya Faɗawa Garba Shehu game da Buhari bayan Ya Ci Zaɓe
- Garba Shehu ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da dama aka gudanar da zaben 2023 cikin adalci da gaskiya
- Ya musanta jita-jitar da ke cewa Buhari bai goyi bayan Bola Tinubu ba, yana mai cewa maganar ba ta da tushe
- A cewarsa, Buhari bai hana kowa takara ba, ya bar kowa ya fafata a zabe cikin 'yanci da dimukuradiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Yayin da ake cigaba da ce-ce-ku-ce kan zaben 2023, Garba Shehu ya kuma yin magana musamman game da abin da ya faru kafin zaben da aka gudanar.
Tsohon hadimin shugaban kasa ya ce Muhammadu Buhari ya taka rawa wurin tabbatar da adalci a zaben da aka gudanar da Bola Tinubu ya yi nasara.

Source: Facebook
Garba Shehu ya fadi yadda suka yi da Tinubu

Kara karanta wannan
A ƙarshe, Garba Shehu ya yi magana kan batun sa wa Buhari 'guba' a AC lokacin mulkinsa
Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata hira da gidan talabijin na Channels a jiya Juma'a 11 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin hirar da aka yi da Garba Shehu ya ƙaryata cewa Buhari bai goyawa Bola Tinubu baya ba inda ya ce shugaban kasa na yanzu da kansa ya fada masa.
Ya ce:
"Ma su fadar haka ina ga a mafarki suke gani, hakan bai faru ba, na fada baya babu wannan magana da ake yadawa.
"Bayan Bola Tinubu ya yi nasara a zabe, ya fada mani cewa Buhari ya ba shi damar cin zaben a yanayin adalci.
"Wannan duk hadin mutane ne, wadanda ke neman gindin zama suna iya fadar komai a gaban shugabanni domin samun abin da suke so."

Source: Twitter
'Kokarin da Buhari ya yi a 2023' - Garba Shehu
Garba Shehu ya ce da Buhari yana son kawo cikas a zaben 2023 da zai iya yi saboda shi ke rike da madafun iko da komai a gwamnati.
Ya ce DSS da sauran jami'an tsaro na karkashinsa kuma zai iya yiwa wasu gwamnoni magana kan abin da yake so a zaɓen amma ya zabi bari a yi cikin adalci.

Kara karanta wannan
Abin ɓoye ya fito fili: An faɗi dalilin rufa rufa kan rashin lafiyar Buhari a mulkinsa
"Buhari yana da jami'an tsaro, zai iya fadawa gwamnoni abin da za su yi amma ya bari aka yi komai yadda ya dace."
Da aka tambayi Garba Shehu me yasa Buhari ya umarci mutane har kusan biyar su nemi takarar shugaban kasa? Sai ya ce:
"To kana tsammanin ya ce musu ka da su nemi takara, duk wanda ya zo wurinsa bai hana shi, kana son takara? Ka nema."
Garba Shehu ya magantu kan jintar Buhari
Kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ya fayyace labarin berayen fadar shugaban kasa a mulkin Muhammadu Buhari.
Garba Shehu ya ce hakan ya zama dabara don karkatar da hankali daga lafiyar Buhari lokacin dawowarsa daga jinya a London da ke kasar Birtaniya.
A cewar Garba Shehu, ya fadi labarin ne bayan wata shawara da aka yi kan wata waya da aka ce beraye sun cinye saboda kawar da hankulan jama'a daga jinyarsa.
Asali: Legit.ng