Wace Irin Cuta Ta Kama Ganduje? An Tsokani Tsohon Gwamnan Kano bayan Ya Karɓi Muƙami a FAAN

Wace Irin Cuta Ta Kama Ganduje? An Tsokani Tsohon Gwamnan Kano bayan Ya Karɓi Muƙami a FAAN

  • Kimanin makonni biyu da suka shige, Abdullahi Ganduje ya yi murabus daga kujerar shugaban APC na ƙasa bisa dalili na rashin lafiya
  • Sai dai ganin yadda cikin ƙasa da makonni biyu ya dawo harkokin siyasa har ya karɓi muƙami a FAAN, wasu ƴan APC sun fara masa shaguɓe
  • Tsohon sanata daga jihar Ekiti, Babafemi Ojudu ya ce yana mamakin wane irin ɗan baiwar likita ne ya iya warkar ɗa Ganduje a ƙankanin lokaci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ekiti - Tsohon sanata kuma jigo a APC, Babafemi Ojudu, ya yiwa tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje, shaguɓe kan yadda ya dawo harkokin siyasa.

Sanata Ojudu ya tsokani Ganduje kan yadda aka gansa a harkokin siyasa ƙasa da makonni uku bayan ya ce rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus daga shugabancin APC.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Garba Shehu ya yi magana kan batun sa wa Buhari 'guba' a AC lokacin mulkinsa

Tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje.
An fara surutu a APC kan yadɗa Ganduje ya dawo harkar siyasa ƙasa da makonni 2 bayan ya ce ba shi da lafiya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Mista Ojudu, wanda ya wakilci Ekiti ta Tsakiya daga 2011 zuwa 2015, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na LinkedIn a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sanata ya yi wa Ganduje shaguɓe

“Ina roƙon shugabanmu, Alhaji Abdullahi Ganduje, da ya fayyacewa ’yan Najeriya irin cutar da ke damunsa wacce ta sa ya yi murabus daga shugabancin APC amma sai gashi ya murmure cikin kasa da makonni biyu," in ji.

Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC a ranar 27 ga Yuni, 2025 a wasiƙar da ya aike wa shugabannin jam'iyyar na ƙasa.

A wasikar, Ganduje ya danganta murabus ɗinsa da batun lafiya, sai dai wasu majiyoyi sun ce akwai rikicin siyasa da zarge-zargen rashawa da suka taimaka wajen yanke wannan shawara.

Wasu mambobin APC sun kai ƙara kan yawaitar neman kuɗi daga ofishin Ganduje musamman masu neman kujerun kansiloli a yankin babban birnin tarayya (FCT).

Kara karanta wannan

Garba Shehu ya fadi halin da Buhari yake ciki bayan kwantar da shi a asibitin Landan

Kasa da makonni biyu bayan murabus da ya danganta da rashin lafiya, sai gashi an nada Ganduje a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwa na Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN).

Wane irin rashin lafiya ke damun Ganduje?

Ojudu, wanda ya kasance mai ba tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, shawara kan harkokin siyasa, ya yi wa Ganduje shaguɓe kan dalilin ja da baya na ɗan lokaci.

Ya ce wataƙila cutar Ganduje ta samo asali ne daga gajiya ta siyasa, hawan jini da shugabanci ya haddasa, ko kuma rashin jituwa da rashin gaskiya da riƙon amana.

Ganduje ya karɓi muƙami a FAAN.
Tsohon sanata kuma jigon APC ya buƙaci Ganduje ya bayyana yadɗa ya warke daga rashin cikin ƴan kwanaki Hoto: @FAAN_Official
Source: Twitter
“Ya kamata mu tambaya, shin gajiya ce ta siyasa? Hawan jini ne da shugabancin jam’iyya ya jawo? Ko kuwa rashin jituwa da rashin gaskiya da amana ne?”
“Abin da yafi ɗaukar hankali, wane ɗan baiwar likita ne ya warkar da Ganduje cikin kankanin lokaci? ’Yan Najeriya na da hakkin su sani."
"Mutane da yawa na fama da rashin lafiya, ina ga ya kamata a faɗa wa ƴan ƙasa wannan magani mai abin al'ajabi domin amfanin ƴan Najeriya."

- Babafemi Ojudu.

An fara rububin kujerar Ganduje a APC

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke tsakanin mutanen Tinubu da Buhari, an fara musayar yawu kan zaben 2015

A wani rahoton, kun ji cewa manyan ƴan siyasa daga Arewacin Najeriya sun fara rububin kujerar shugabancin APC bayan Ganduje ya yi murabus.

Ana rade radin manyan 'yan siyasa da suka hada da Tanko Al-Makura, Joshua Dariye da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello suna cikin masu neman kujerar.

A ranar 25 ga watan Yuli, za a yi taron babban kwamitin zartarwa (NEC) na APC wanda ake sa ran zaɓar wanda zai karɓi ragamar jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262