'Yan Najeriya Sun Fara Nuna Wanda Suke So Haɗakar ADC Ta Tsayar Takara a 2027
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya fara samun goyon baya a shirinsa na neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar haɗaka watau ADC
- Kungiyar mazauna yankin da ke samar da mai a Neja Delta ta ayyana goyon bayanta ga Amaechi, tana mai cewa shi ya dace ya karɓi Najeriya
- Shugaban ƙungiyar, Joseph Ambakaderimo ya ce bai kamata ADC ta ba Atiku takara ba har sai Kudu ta gama shekara takwas
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger Delta - Yayin da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 ke ƙara kankama, al'ummar yankunan da ke samar da mai da gas a Neja Delta sun shiga haɗakar ADC.
Mazauna yankin Neja Delta sun kuma bayyana tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin ɗan takararsu na zaɓen shugaban ƙasar 2027 a inuwar ADC.

Kara karanta wannan
ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

Source: Facebook
Sun kuma roki haɗakar jam'iyyun adawa da ta rungumi ADC ta tsayar da Amaechi takara a zabe mai zuwa domin ceto Najeriya, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amaechi ya fara samun goyon baya a ADC
Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar raya yankin da ke samar da mai da gas a Neja Delta (CDC), Joseph Ambakaderimo, ne ya faɗi hakan a Fatakwal yau Juma'a.
Ya yabawa Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai ƙwarewa, jarumta, da karɓuwa a faɗin ƙasa.
Ambakaderimo ya bayyana cewa gogewar siyasa da Amaechi ke da ita, duba da muƙaman da ya rike, ya sanya shi ya fi sauran masu neman takara a haɗakar ƴan hamayya.
Amaechi dai ya riƙe kujerar kakakin Majalisar Dokokin Ribas, ya yi gwamna na tsawon zango biyu a Ribas, sannan ya shafe shekara takwas a matsayin ministan sufuri.
Ƴan Neja Delta sun marawa Amaechi baya
“Gogewar siyasa da jarumtar Amaechi wajen fuskantar matsalolin ƙasa na tsawon shekaru sun sa ya zarce duka masu neman takara. Shi jarumi ne kuma ya tabbatar da cancantarsa.
"Ayyukan da ya yi a Jihar Ribas da lokacin da ya kasance Minista karkashin Shugaba Muhammadu Buhari sun isa shaida.”
- Joseph Ambakaderimo.
Shugaban CDC ya jaddada cewa idan jam’iyyun hamayya na da niyyar kawar da Shugaba Bola Tinubu a 2027, to Amaechi ne zaɓi mafi kyau.
Ya ƙara da cewa Amaechi yana da farin jiki da karɓuwa a faɗin ƙasa, musamman a Arewa, inda ya “aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba lokacin da yake Minista."

Source: Facebook
An fara juyawa Atiku baya a haɗakar ADC
Ambakaderimo ya nuna rashin gamsuwa da ba Atiku Abubakar tikitin takarar shugaban ƙasa a ADC, yana mai cewa ƴan Najeriya sun fi karkata kan mulki ya ci gaba da zama a Kudu
"Hakika, Peter Obi ya yi fice a 2023, amma Amaechi ya nuna ƙarfinsa lokacin zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC, inda ya zo na biyu bayan Bola Tinubu,” in ji shi.
Aregbesola ya hango abinda zai ba ADC nasara

Kara karanta wannan
Lukman ya rabawa Atiku da Obi gardama, ya faɗi wanda ADC za ta tsayar takara a 2027
A wani labarin, kun ji cewa tsohon aminin Tinubu kuma tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ya ce idan ƴan adawa suka yi haɗaka ba mai iya soke su a zaɓe.
Aregbesola, wanda ya rike kujerar ministan cikin gida a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya ce haɗakar ƴan adawa ta shirya ƙalubalantar Tinubu.
Ya ce jam’iyyar ADC na gina wani babban ƙawance da ke haɗa ’yan Najeriya masu kishin ƙasa don ceto Najeriya daga gurɓataccen shugabanci.
Asali: Legit.ng
