Kashim Shettima Ya Caccaki Tinubu kan Dakatar da Fubara? An Samu Gaskiya

Kashim Shettima Ya Caccaki Tinubu kan Dakatar da Fubara? An Samu Gaskiya

  • Fadar shugaban kasa ta karyata rahotannin da ke cewa Mataimakin Shugaba Shettima ya soki Bola Tinubu kan dakatar da gwaman Rivers
  • Shettima ya yi bayanin tarihi ne kawai game da mulkin Goodluck Jonathan, ba wani tsokaci ba ne kan rikicin siyasa a jihar Rivers ba
  • Fadar shugaban kasa ta jaddada cewa babu rabuwar kai tsakanin Tinubu da Shettima, ta kuma bukaci 'yan jarida su guji yada labaran karya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi martani kan rahotanni da ake yadawa cewa Kashim Shettima ya fada a taro.

Fadar ta karyata ikirarin da ke cewa Shettima ya soki Shugaba Tinubu kan dakatar da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara.

An fayyace kalaman Shettima kan rigimar Rivers
An karyata cewa Shettima ya caccaki Tinubu kan rigimar Rivers. Hoto: Kashim Shettima, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

An kare kalaman Kashim Shettima a taro

Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin Shettima a ɓangaren sadarwa, Stanley Nwokocha ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura Shettima London duba lafiyar Buhari da ke kwance a asibiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce rahoton da ake danganta Shettima da su ƙarya ne an juya maganganunsa ne.

Ta bayyana maganganun Shettima na tarihi ne dangane da abubuwan da suka faru a lokacin mulkin Jonathan, ba su da alaƙa da al'amuran yanzu.

Fadar shugaban kasa ta sake jaddada haɗin kai tsakanin Tinubu da Shettima, ta kuma ja kunnen kafafen yaɗa labarai da su daina yada labaran da ke haddasa tashin hankali.

Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa an yi kuskuren haɗa maganganun Shettima da batun dakatar da Fubara a Rivers.

Shettima ya yi jawabi ne a wajen kaddamar da littafin OPL 245: 'The Inside Story of the $1.3 Billion Oil Block' a Abuja, ranar Alhamis 10 ga Yuli, 2025.

An kare Shettima kan kalamansa a taro
An karyata cewa Shettima a caccaki Tinubu kan dakatar da Fubara. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Zargin yi wa Shettima karya a rahotanni

Wasu kafafen yaɗa labarai sun fassara misalin da Shettima ya bayar na yunkurin tsige shi a matsayin cin fuska ga Tinubu dangane da Rivers.

Kara karanta wannan

'Mun gane wayon': ADC ta yi martani kan zargin shiryawa Tinubu 'juyin mulki'

Sanarwar da Stanley Nkwocha ya sa wa hannu ta ce:

“Maganganun Shettima na ilimi ne kawai, sun yi nuni da ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya.
“Ya yi bayanin abubuwan da suka faru ne a mulkin Jonathan, ba tsokaci ba ne kan abubuwan da ke faruwa yanzu.”

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Tinubu bai cire Gwamna Fubara ba, sai dai ya amince da dakatar da shi na ɗan lokaci saboda matsalar tsaro.

Ta ambato sashe na 305 na kundin tsarin mulki da ke bai wa Shugaba damar ɗaukar matakin dokar ta-baci.

“Rikicin Rivers ya kai matakin da ya zama dole a dakatar da wasu jami’an jiha domin hana rikice-rikicen siyasa da barazana ga jama’a.”

- Cewar sanarwar

Fadar shugaban kasa ta ce rahotannin da ke cewa akwai sabani tsakaninsu ba su da tushe, kuma suna cutar da ƙasa.

Shettima ya sharci jam'iyyun siyasa a Najeriya

Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi magana kan jam'iyyun adawa a wani taro a Abuja a ranar Alhamis 10 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Littafi: Garba Shehu ya tara Gowon, Atiku, Osinbajo, El Rufa'i, Aminu Ado a Abuja

Shettima ya ce duk ‘yan siyasa daya suke wajen gina kasa, komai bambancin jam’iyyarsu da ra’ayinsu na siyasa.

Shettima ya bayyana haka zaman taron kaddamar da littafi da ya haɗa da ‘yan siyasa daga APC, PDP, NNPP da ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.