ADC: An Fara Ƙoƙarin Canza Wa Atiku Tunani, Haɗaka na Fuskantar Gagarumar Matsala

ADC: An Fara Ƙoƙarin Canza Wa Atiku Tunani, Haɗaka na Fuskantar Gagarumar Matsala

  • Bode George ya fara rarrashin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubukar da sauran kusoshin PDP da suka shiga tafiyar haɗaka
  • Tsohon mataimakin shugaban PDP ya buƙaci su dawo su zauna a jam'iyyar domin sake ginata, ta dawo kan ganiyarta
  • George ya yi ikirarin cewa babu wata haɗakar ƴan adawa da za ta iya zarce PDP ƙarfi, inda ya roƙi su tuna da gatan da jam'iyyar ta masu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban PDP a ƙasa, Olabode George, ya yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar, Sanata David Mark da sauran jiga-jigai su haƙura su zauna a jam'iyyar.

Geroge ya rarrashi Atiku da sauran manyan kusoshin PDP da ke shirin haɗewa da ADC su canza tunani, su dawo cikin babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa domin a haɗa kai.

Kara karanta wannan

Tsohon jigo a PDP ya gano babbar matsalar jam'iyyar gabanin zaben 2027, "Atiku ne"

Tsohon mataimakin shugaban PDP, Bode George.
Bode Geroge ya buƙaci Atiku da sasu ƙusoshin PDP su sauya tunani kan shiga haɗaka Hoto: Bode George
Source: Facebook

Chief Bode George ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a ofishinsa da ke Ikoyi, Legas, a ranar Alhamis, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

George ya yi ikirarin sasanta rikicin PDP

Ya ce sun yanke shawarar gudanar da wannan taro ne domin zaman lafiya ya dawo cikin PDP, kuma a warware sabanin da ke cikin jam’iyyar don amfaninta gaba ɗaya.

Ya bayyana cewa rikicin da ke matakin ƙasa yanzu ya ƙare, sannan ya yi kira ga waɗanda ke yunƙurin kafa wani haɗin gwiwa su dawo cikin PDP, yana mai cewa babu wata haɗaka da za ta fi ƙarfin PDP.

Chief George ya ce PDP jam’iyya ce da aka sake farfado da ita, wadda ta jure wa kalubale da dama, kuma ba za a iya rushe ta ba.

PDP ta fara koƙarin canza tunanin su Atiku

Ya ƙara da cewa waɗanda ke ƙoƙarin barin jam’iyyar domin kafa haɗaka kamar su na yi wa kabarin waɗanda suka kafaPDP fitsari ne, bayan sun sadaukar da rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Lukman ya rabawa Atiku da Obi gardama, ya faɗi wanda ADC za ta tsayar takara a 2027

A cewarsa, hakan babban rashin adalci ne ga jam’iyyar PDP, wacce kusan dukansu suka hau dandalinta suka kai matakin da suka kai a ƙasar nan.

Bode George ya ce sun taɓa bin wannan hanyar a baya amma ba ta haifar da da mai ido ba, yana mai cewa zai fi kyau su ci gaba da zama a PDP don taimakawa wajen gina ta.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
George ya ce PDP ta warware rikicin da ya dabaibaye ta Hoto: @Atiku
Source: Facebook

A rahoton Vanguard, tsohon jagoran PDP ya ce:

"PDP ta jure wa hadurran siyasa, yanzu an sake dawo da ita kan turba. Ya kamata mutanen da suka kai manyan mukamai a Najeriya ta dalilin jam’iyyar, su sake tunani, su yi hankali, babu wata haɗaka da za ta fi ƙarfin PDP.”

ADC ta shirya karɓe mulki daga APC a 2027

A wani labarin, kun ji cewa sakataren rikon kwarya na jam’iyyar ADC kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya yi ikirarin cewa ƙarshen APC ya zo.

Sai dai Aregbesola ya ce dole ne ƴan haɗakar jam'iyyun adawa su haɗa kansu wuri guda, idan suna son samun nasara a zaɓukan 2027.

Aregbesola, wanda ya rike kujerar ministan cikin gida a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya ce haɗakar ƴan adawa na ci gaba da samun goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262