ADC Ta Yi Martani kan Maganar yi wa Tinubu Juyin Mulki a Najeriya

ADC Ta Yi Martani kan Maganar yi wa Tinubu Juyin Mulki a Najeriya

  • Jam’iyyar ADC ta ce ba ta da wata niyyar kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar juyin mulki ko wani salo da ya sabawa dimokuradiyya
  • Kakakin rikon kwarya na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya ce kuri’a suke da ita ba alburusai ba, kuma za su fafata da APC ne ta hanyar zabe
  • Bolaji Abdullahi ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da hadimansa daga yada zarge-zargen da ka iya haddasa hargitsi a kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jam’iyyar ADC ta karyata zargin da wani hadimin shugaban kasa ke yi cewa jam’iyyun adawa na shirin kifar da gwamnatin Bola Tinubu kafin 2027.

Kakakin rikon kwarya na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Mun gane wayon': ADC ta yi martani kan zargin shiryawa Tinubu 'juyin mulki'

ADC ta musa shirin kifar da gwamnatin Tinubu
ADC ta musa shirin kifar da gwamnatin Tinubu. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya yi magana yana mai cewa jam’iyyarsu ta tsai da kudurin karɓar mulki ne ta hanyar dimokuradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan martanin na ADC na zuwa ne bayan wata maganar da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya yi, inda ya zargi 'yan adawa da shirin kifar da gwamnati.

"Ba sojoji ba ne mu" – ADC da Tinubu

Bolaji ya ce jam’iyyar su ba sojoji ba ne, kuma ba su da makami ko alburusai, sai dai suna da kuri’un al’umma da zasu dogara da su wajen fitar da APC.

Daily Trust ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya ce:

“Mu ba sojoji ba ne, mu ‘yan siyasa ne. Ba mu da alburusai sai kuri’u.
"Idan lokacin ya yi, za mu gabatar da manufofinmu ga Najeriya, sannan mu bar ‘yan kasa su yanke hukunci,”

Ya kara da cewa zargin Onanuga ba gaskiya ba ne, illa dai wata hanya ce da wasu ke amfani da ita wajen danne ‘yancin 'yan adawa da hana su fadin albarkacin bakinsu.

Kara karanta wannan

ADC ta gano yadda ake damfarar yan Najeriya da sunanta, ta tura gargadi ga jama'a

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

"APC ta manta da lokacin da ta yi adawa,' ADC

Kakakin ADC ya ce abin mamaki ne yadda jam’iyyar APC, wacce ta hau mulki na farko a matsayin 'yar adawa a 2015, yanzu tana ganin tamkar laifi ne mutum ya zama dan adawa.

Ya bukaci Tinubu da ya ja kunnen hadimansa da su daina yada irin wadannan zarge-zargen da ka iya tada tarzoma, duba da cewa har yanzu saura shekaru biyu a kai ga babban zabe.

ADC ta ce tana bin hanyar dimokuradiyya

Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyarsu za ta ci gaba da bin hanyar lumana da dimokuradiyya domin ciyar da kasa gaba.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ki yarda da duk wani yunkuri da zai hana adawa fadin albarkacin bakinsu ko hana su shiga fafatawa a siyasa.

Ribadu ya gargadi 'yan adawa a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya soki 'yan adawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan zargin badakala, Peter Obi ya fadi alakar da ta hada shi da Abacha

Nuhu Ribadu ya ce 'yan adawar da suke sukar gwamnati ne suka hana ruwa gudu a Najeriya a lokacin da suka samu dama.

Baya ga haka, Ribadu ya ce shugaban kasa Bola Tinubu na kokarin kawo sauyi a Najeriya musamman a fannin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng