"Akwai Jan Aiki a Gabanmu," Tsohon Aminin Tinubu Ya Hango Abin da Zai Karya APC a 2027
- Tsohon aminin Tinubu kuma tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ya ce ADC za ta iya kawo ƙarshen mulkin APC idan ƴan adawa suka haɗa kai
- Aregbesola, sakataren ADC na ƙasa ya ce sun shirya haɗa ƙawance mai ƙarfi da zai ƙalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027
- Tsohon gwamnan na jihar Osun ya ce matukar ƴan hadakar ADC suka haɗa kansu, babu wanda ba za su iya kayarwa ba a zaɓe
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo - Sakataren rikon kwarya na jam’iyyar ADC kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa ƙarshen APC ya zo matuƙar ƴan adawa suka haɗa kai.
Aregbesola, wanda ya rike kujerar ministan cikin gida a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya ce haɗakar ƴan adawa za ta kawar da mulkin APC a 2027.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai

Source: Facebook
Ya faɗi hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Akure, babban birnin jihar Ondo, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ADC ke shirin kifar da APC a 2027
Aregbesola ya ce jam’iyyar ADC na gina wani babban ƙawance da ke haɗa ’yan Najeriya masu kishin ƙasa don kalubalantar mulkin Shugaba Bola Tinubu.
A cewarsa:
"Mu jingine burikanmu, mu haɗa kai wuri guda. Zaɓuka da dama suna gabatowa, na shugaban ƙasa, majalisar dokoki da na jihohi, wanda idan muka haɗa kai babu mai iya doke mu.
Aregbesola ya jaddada cewa jam’iyyar ADC na samun gagarumar goyon baya daga fitattun jagororin ’yan adawa, kamar Atiku Abubakar da Peter Obi.
Aregbesola ya hango abin da APC ke shiryawa
Ya kuma ja kunnen mambobin haɗaka da su shiryawa farfaganda daga APC, wadda ya ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen tarwatsa wannan haɗaka ta ƴan adawa.

Kara karanta wannan
"Zai iya kifar da Tinubu," Momodu ya faɗi wanda ya dace ADC ta tsayar takara a 2027
Ya bukaci magoya bayan jam’iyyar ADC da su ci gaba da mayar da hankali kan babban aiki da ke gabansu, su guji shisshigi ko tayar da rikicin cikin gida.
A nasa jawabin, Hon. Gbenga Edema, tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar Ondo, ya zargi APC da ƙirƙiro farfaganda don zubar da mutunci da haifar da rlrikici don ruguza ADC.
“Shari’o’in da ke gaban kotu da ake ta yadawa kawai jan hankali ne. Ba su da tasiri kan harkokin siyasar mu.”

Source: Twitter
Ƴan ADC sun koka kan halin da Najeriya ke ciki
Tsohon jigon APC kuma tsohon hadimin gwamna, Hon. Akin Akinbobola, ya nuna damuwarsa kan halin da ƙasa ke ciki, yana mai kira ga duk masu kishin ci gaba da su shiga haɗaka don "ceto Najeriya daga halin da ta shiga."
A cewarsa:
“Najeriya na cikin mawuyacin hali, rashin tsaro da yunwa sun zama ruwan dare. ADC ta shirya dawo da fata mai kyau a tsakanin ƴan ƙasa."
ADC ta gargaɗi Atiku, Peter Obi da Amaechi
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar hadaka ta ADC ya gargaɗi Atiku, Peter Obi da sauran masu shirin neman takarar shugaban ƙasa a inuwarta.
Jam’iyyar ta bayyana cewa ba za ta fifita kowa ba yanzu, domin akwai bukatar a gina jam’iyyar da kyau kafin a fara batun shugabanci.
Shugaban rikon kwarya na ADC na kasa, Sanata David Mark ne ya yi gargadin ganin yadda ake kara samun cece-kuce dangane da zaben.
Asali: Legit.ng
