2027: Malamin Addini Ya Faɗi Tikitin Mutum 2 Kacal da Zai Iya Kayar da Tinubu cikin Sauƙi
- Fasto Adewale Giwa ya ce tikitin hadin guiwa tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi kadai zai iya kayar da Bola Tinubu a 2027
- Ya jaddada cewa dole Obi ya janye ya mara wa Atiku baya, domin samun kuri’un Arewa da fuskantar jam’iyyar mai mulki
- Giwa ya ce Atiku zai iya mika mulki wa dan Kudu maso Gabas, amma yanzu ba za a bar dan yankin ya ci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Faston Babban Cocin The Second Coming of Christ Ministry, Adewale Giwa ya yi magana kan yadda za a kayar da Bola Tinubu.
Giwa ya bayyana cewa tikitin hadin gwiwar Atiku Abubakar da Peter Obi karkashin jam’iyyar ADC ne kadai zai iya kayar da Shugaba Tinubu a 2027.

Source: Twitter
An fadi masu kayar da Tinubu a 2027
Yayin da yake zantawa da Daily Post, malamin addinin ya ce Obi na iya samun kuri’u daga Arewa kamar yadda Atiku zai iya janyo kuri’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto Giwa ya bayyana cewa za a sha kaye idan Obi ya ki janyewa Atiku domin ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ADC.
Ya ce:
“Tikitin zai fi kyau idan Atiku da Obi sun hade, tikitin Atiku da Obi kadai zai iya kayar da jam’iyya mai mulki.
"Idan aka zabi Obi ya tsaya takara a madadin kawancen, bana ganin nasara ga jam’iyyar kawancen.
“Tikitin Atiku-Obi ne kadai zai kayar da Tinubu domin ba zai samu goyon bayan Arewa ba, ko Kudu, sai kawai daga Kudu maso Gabas.”

Source: UGC
Fasto ya fadi tasirin Atiku, Obi a 2027
Fasto Giwa ya kara da cewa Atiku zai iya mika mulki ga dan Kudu maso Gabas idan ya zama shugaban kasa a zaben 2027.
Ya kara da cewa:
“Idan Atiku ya zama shugaban kasa na gaba, na tabbata zai fi dacewa ya mika mulki ga yankin Kudu maso Gabas."
Ya jaddada cewa ba za a bar dan Kudu maso Gabas ya lashe zabe a yanzu ba, ko da yana da karbuwa da farin jini.
“A yadda al’amura ke tafiya, idan wani daga Kudu maso Gabas ya fito takara da jam’iyya mai mulki, ba za su bar shi ya ci ba.
“Idan Obi ya hakura ya tsaya a ƙarƙashin Atiku, za su iya samun nasara a 2027.
"Watakila Obi zai so ya janye la’akari da sakamakon zaben baya, tunda ya san Atiku ya fi shi karfi da farin jini.
“Obi zai yarda domin da bai da niyyar janyewa ba da bai shiga kawancen ba. Ya san Atiku ya fi shi karfi, kuma hakan zai taimaka wa Najeriya.”
- Cewar Fasto Giwa
'Jonathan ne kadai zai kayar da Tinubu'
Mun ba ku labarin cewa wasu mazauna Jalingo da ke jihar Taraba sun bukaci ADC ta tsayar da Goodluck Jonathan takara a 2027.
Sun ce Jonathan na da karbuwa a Arewa da Kudu, kuma zai tsaya wa wa’adin mulki daya kacal wanda ya fi jan hankalin Arewa.
Masu magana sun jaddada cewa Jonathan zai kawo sauyin tattalin arziki, kuma su na bukatar ADC ta daina son kai ta mai da hankali kan nasara.
Asali: Legit.ng


