Kotun Kolin Najeriya Ta Raba Gardama kan Batun Tsige Gwamnan APC daga Mulki

Kotun Kolin Najeriya Ta Raba Gardama kan Batun Tsige Gwamnan APC daga Mulki

  • Kotun koli ta kori karar da ɗan takarar gwamnan PDP a zaɓen jihar Edo, Asue Ighodalo ya ƙalubalanci nasarar Gwamna Monday Okpebholo
  • Kwamitin alkalai biyar ya yanke hukuncim cewa babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da za ta sa a soke sakamakon zaben Edo da aka yi a watan Satumba, 2024
  • Sanata Monday Okpebholo na jam'iyyar APC ne ya samu nasara a zaɓen bayan doke PDP mai mulki a wancan lokacin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kotun Koli a Najeriya, a ranar Alhamis ta tabbatar da nasarar zaɓen Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo.

Hakan dai na kunshe ne a cikin hukunci da kwamitin alkalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ya yanke yau Alhamis a Abuja.

Gwamnan Edo da ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo.
Kotun Kolin Najeriya ta warware duk wani ƙorafi game da nasarar gwamnan Edo Hoto: Asue Ighodalo, @MAkpakomiza
Source: Facebook

Kotun Ƙoli ta kori ƙarar Asue Ighodalo

Kara karanta wannan

Kudirin ƙirƙiro karin jiha 1 a Arewacin Najeriya ya samu gagarumin goyon baya a Majalisa

Kotun Koli ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo, ya shigar yana neman a tsige Gwamna Okpebholo, kamar yadda Vanguard ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar PDP ya roki a soke sakamakon zaɓen gwamnan da aka gudanar a jihar Edo ranar 21 ga Satumba, 2024

Kotun ta ce babu wata hujja da za ta sa ta soke hukuncin da Kotun Daukaka Kara da kuma Kotun Sauraron Kararrakin Zaɓen Gwamnan Edo suka yanke.

Duka kotunnan guda biyu dai sun tabbatar da cewa Okpebholo na jam’iyyar APC ne sahihin wanda ya lashe zaɓen Edo.

Hukuncin kotun ya tabbatar da nasarar APC

Kotun Ƙoli ta bayyana cewa mai ƙara, wato Ighodalo, bai gabatar da hujjoji masu inganci da shari’a ta yarda da su don tabbatar da zargin da ya yi cewa zaɓen cike yake da kura-kurai ba.

Haka kuma, Kotun ta ce mai ƙarar bai kira shaidu masu muhimmanci da za su bayyana yadda wasu daga cikin abubuwan da ya gabatar suka faru ba, musamman game na’urorin tantance masu zaɓe na BVAS.

Kotun ta ce wasu daga cikin hujjojin da aka miƙa (ba tare da shaida ba) ba a tabbatar da su ba a rumfunan zaɓe 432 daga cikin jimillar 4,519 da ke faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Tsohon makusancin Obi ya fadi yadda ADC za ta mikawa Tinubu nasara a 2027

Ɗan takarar PDP ya gaza gabatar da hujjoji

“Mai ƙara bai cika sharuɗɗan dokar kasa ta dora masa na tabbatar da ƙorafinsa ba,” in ji Kotun Koli cikin hukuncin da Mai Shari’a Garba ya karanta.

Tun farko, Ighodalo dai ya roƙi Kotun Ƙoli, a ƙara mai lamba SC/CV/536/2025, da ta soke hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a ranar 29 ga Mayu na watsi da ƙarar da ya shigar tare da tabbatar da nasarar Gwamna Okpebholo.

Gwamma Monday Okpebholo.
Kotun koli ta ce ɗan takarar PDP ya gaza gabatar da hujjoji Hoto: Monday Okpebholo
Source: Facebook

Sai dai kotun koli, mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta ce babu dalilin soke wannan hukunci, saboda mai ƙara ya gaza gabatar da kwararan hujjoji, rahoton Channels tv.

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Okpebholo ya sha alwashin bai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kuri’a miliyan 2.5 a zaɓen 2027.

Monday Okpebholo ya ce zai yi haka ne a matsayin wata hanya ta nuna godiya ga Shugaba Tonubu bisa yadda yake ƙauna da kulawa da jihar Edo.

A cewarsa, idan aka fita filin zaɓe a 2027, za a gane irin goyon bayan da ƴan Najeriya ke yi wa shugaban ƙasa da gwamnatin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262