APC: 'Yan Siyasar Arewa Sun Fara Neman Kujerar Ganduje Gadan Gadan
- Sanata George Akume, na cikin manyan 'yan takara da ake hasashen na zawarcin kujerar shugaban jam'iyyar APC na kasa
- Ana rade radin 'yan siyasa da suka hada da Tanko Al-Makura, Joshua Dariye da Yahaya Bello suna cikin masu neman kujerar
- An fara magana kan kujerar tun bayan murabus din Abdullahi Ganduje a watan Yuni, yayin da NEC ke shirin taro a ranar 25 ga Yuli
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Taron babban kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC da ke tafe a ranar 25 ga Yuli ya sanya manyan 'yan siyasa da dama fara fafutukar neman kujerar shugaban jam’iyyar na kasa.
Bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabanci a watan Yuni, ‘yan takara daga yankin Arewa ta Tsakiya sun fara jan hankalin jiga-jigan jam’iyyar da kuma mambobin NEC.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa wasu fitattun jiga-jigan APC sun fara ganawa da shugabanni da wakilan jam’iyya domin karfafa takararsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabancin APC: Akume na kan gaba
An ce daga cikin fitattun 'yan takarar akwai tsohon gwamnan jihar Benue, George Akume, wanda ke rike da kujerar sakataren gwamnatin tarayya a yanzu.
Akume ya taba neman shugabancin APC a 2022 amma ya janye saboda bukatar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wasu majiyoyi na APC sun bayyana cewa ana kallon Akume a matsayin wanda zai samu kujerar saboda kusancinsa da Bola Tinubu.
Tanko Al-Makura da tsofaffin jiga-jigan CPC
Sanata Tanko Al-Makura, da ya taba neman kujerar shugabancin APC a baya, yana samun goyon bayan tsofaffin mambobin CPC da ke bukatar a mayar da kujera yankin Arewa ta Tsakiya.
Shugaban kungiyar matasan jihohi na tsohuwar CPC, Sani Salisu, ya nemi a bai wa Nasarawa damar sake rike wannan kujera, yana mai cewa Al-Makura ya cancanta da kujerar.

Source: Facebook
Dariye, Yahaya Bello da Sani Musa
Wasu na goyon bayan tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, wanda suka ce yana da gogewa tun lokacin da Tinubu ke gwamna a Legas.
Haka nan, an ce Sanata Sani Musa da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, na samun goyon bayan matasa da ke kallon su a matsayin sababbin jini da ke da fahimtar zamani.
Gemade da sauran jiga-jigan siyasa
Sanata Barnabas Gemade, wanda ya taba shugabantar PDP, yana da goyon bayan wasu ‘yan jam’iyya daga Benue.
Shugaban karamar hukumar Tarka, Raphael Yenge, ya ce bai kamata matsayin Akume na SGF ya hana wani daga Benue neman shugabancin APC ba.
Yenge ya bayyana cewa:
“Sanata Gemade dattijo ne da ke da kwarewa sosai, kuma zai iya dawo da hadin kai da karfin jam’iyya kafin 2027.”
Kokarin da Mohammed Etsu ke yi
Mohammed Etsu da ya taba neman kujerar a 2022, ya kafa wata kungiya domin karfafa bukatar yankin Arewa ta Tsakiya.
Ya ce sun fara tuntubar dattawa, matasa da shugabanni daga sassa daban-daban domin fitar da dan takara daya da zai hada kai da shugabannin kasa da na jam’iyya.
Ganduje ya fara aiki a hukumar FAAN
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya fara aiki a hukumar FAAN.
A ranar Laraba ne ministan sufurin jiragen saman Najeriya ya gabatar da Ganduje a matsayin shugaban hukumar gudanarwar FAAN.
Hakan na zuwa ne bayan Abdullahi Ganduje ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC na kasa saboda dalilan rashin lafiya.
Asali: Legit.ng


