ADC Ta Gano Yadda ake Damfarar Yan Najeriya da Sunanta, Ta Tura Gargadi ga Jama'a

ADC Ta Gano Yadda ake Damfarar Yan Najeriya da Sunanta, Ta Tura Gargadi ga Jama'a

  • Jam’iyyar ADC ta ce labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta na nada shugabannin jihohi ba gaskiya ba ne
  • Jam’iyyar ta bukaci jama'a su tabbatar da duk wani bayani daga jam’iyyar ta hanyar bibiyar shafin kakakinta, Bolaji Abdullahi
  • Haka kuma ADC ta yi karin haske a kan bayar da kudi domin yiwa yan kasa rajistar zama cikakken yayan jam'iyya da wasu ke yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Jam’iyyar hadakar adawa ta ADC ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa an nada shugabannin jam’iyyar a jihohi 36 da Abuja.

Wasu rahotanni da aka fitar a baya sun jerin sunayen wadansu mutane da kowanne aka bayyana shi da shugaban ADC a daya daga cikin jihohi kasar na.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fara gargadin ƴaƴanta kan takarar shugaban ƙasa bayan hadaka

ADC ta gargadi jama'a
ADC ta ƙaryata jerin sunayen shugabanninta a jihohi Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Amma wata sanarwa da Mukaddashin mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya wallafa a shafinsa na X ta karyata labarin, inda ta ce ba shi da tushe.

ADC ta gargadi jama'a

Jam’iyyar ADC ta bukaci jama’ar Najeriya da su rika tantance duk wata sanarwa daga jam’iyyar ta hanyar bin sahihan hanyoyin sadarwarta.

Malllam Bolaji Abdullahi ya ce sahihan hanyoyin sun hada shafin X na mai magana da yawunta na kasa, @BolajiADC. A cewarsa, duk wata sanarwa da ba ta fito daga sahihan hanyoyin sadarwarta ba, kuma ba a tabbatar da ita a shafin X na kakakinta na kasa ba, ka da a dauke ta da muhimmanci.

Bolaji Abdullahi ya nanata cewa duk wani bayani kan harkokin jam’iyyar da hadin guiwar da take yi da wasu kungiyoyi za a fitar da su ne ta sahihan hanyoyin da aka amince da su.

Ya ce:

“Jam’iyyar ADC na kira ga ‘yan Najeriya da su rika tabbatar da duk wani bayani da ya shafi jam’iyyar ta hanyar duba shafin X (Twitter) na Kakakin Yada Labaranta na Kasa, @BolajiADC.”

Kara karanta wannan

2027: ADC a Kudancin Najeriya ta fadi matsayarta kan tsayar da Atiku takara

ADC ta ƙaryata rajista da kudi ga jama'a

Mai magana da yawun jam’iyyar ya kuma bayyana damuwa kan wasu shafukan bogi da ke karbar kudi daga hannun jama’a da sunan rajistar shiga jam’iyyar ta hanyar intanet.

An musanta jerin sunayen yan ADC
ADC ta ƙaryata fara rajista da kudi Hoto: ADC Coalition 2027
Source: Twitter

Ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta amince da kowanne tsarin biyan kudi ta yanar gizo don rajista ba, yana mai bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na damfara da yaudara.

A cewarsa:

“Jam’iyyar ADC ta karyata kuma ta la’anci yadda wasu mutane ke amfani da shafukan yanar gizo na bogi don karbar kudi daga hannun ‘yan Najeriya da sunan rajistar shiga jam’iyyar.”

Ya shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan tare da tabbatar da cewa suna samun bayanai daga sahihan hanyoyi kafin su yarda da kowanne bayani da ya shafi ADC ko hadakar jam’iyyun adawa.

ADC ta yi martani ga fadar shugaban kasa

A wani labarin, kun ji cewa Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da yin shiru da gangan kan wahalhalun 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya zama jagoran ADC a Jigawa, an fara gangami

Jam’iyyar ta ce sabbin shirye-shiryen gwamnati, musamman wadanda suka shafi farfado da samar da abinci mai yawa ga talakawa sun tabbatar da zarginta.

A cewar ADC, kafuwarta da ƙara ƙarfi a kwanakin nan ya gigita Shugaba Tinubu, har ta sa gwamnatin ta soma nuna damuwa a kan halin da talakawa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng