Lukman Ya Rabawa Atiku da Obi Gardama, Ya Faɗi Wanda ADC Za Ta Tsayar Takara a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban APC, Salihu Lukman ya ce har yanzu ADC ba ta fara maganar tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa ba
- Lukman, wanda yana daya daga cikin jagororin haɗaka ya ce jam'iyyar za ta shirya zaben fidda gwani na gaskiya da adalci
- Ya buƙaci magoya bayan Peter Obi, Atiku Abubakar da sauran masu neman takara su yi adawa mai tsafta, su marawa duk wanda ya samu nasara baya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗaya daga cikin jagororin jam’iyyar haɗaka ADC, Mallam Salihu Lukman, ya bayyana cewa ba su fara tattaunawa kan takarar shugaban ƙasa a 2027 ba.
Sai dai Lukman ya jaddada cewa haɗakar ADC za ta fitar da ɗan takararta ne ta hanyar zaɓen fidda gwani na gaskiya da adalci, yana mai cewa babu wanda za a ba fifiko.

Source: Twitter
Salihu Lukman, tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa (Arewa maso Yamma) ya faɗi haka ne a wata hira da ya yi da Channels tv da safiyar ranar Talata.
Yadda haɗakar ADC za ta fitar da ɗan takara
Ya bayyana cewa duk wanda ya samu nasarar zama ɗan takarar jam’iyyar, za a mara masa baya gaba ɗaya domin guje wa kurakuran da suka faru a baya.
Lukman ya yi kira ga magoya bayan manyan jagororin adawa daban-daban da suka hade da ADC su dunƙule su zama tsintsiya ɗaya domin ceto Najeriya.
Ya ce da idan aka bari shugabannin adawa suka rabu, hakan kamar ba wa APC da Shugaba Bola Tinubu nasara ne kai tsaye.
Lukman da roki magoya bayan Obi da Atiku
"Saboda haka, mu kiyaye, mu tabbatar da cewa mun yi adawa a cikin haɗin kai. Kuma idan muna son a samu haɗin kai, ba muna nufin wani ya janye ba ne.”

Kara karanta wannan
Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai
“Ina kuma roƙon 'yan Obi da sauran ƙungiyoyi da su fahimci cewa ADC da haɗakar da aka kafa ita ce mafakar su, su zo mu gina kanmu tare.”
“Idan Peter Obi ya samu nasarar zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, za mu mara masa baya gaba ɗaya mu ƙarfafa shi domin guje wa matsalolin da suka faru a baya.
"Haka zalika, idan Atiku Abubakar ne ya samu nasara, za mu goyi bayansa kuma mu karfafa shi domin kada ya maimaita kura-kuran da tsohon Shugaba Buhari ya aikata.”
- Salihu Lukman.

Source: Facebook
Jam'iyyar ADC za ta ba kowane mamba dama
A cewarsa, ADC za ta yi kokarin kwatanta adalcI da daidaito a cikin duka shawarwarin da za ta ɗauka, inda ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta ba kowa dama.
Lukman ya kuma jaddada cewa har yanzu ADC ba ta yanke hukunci game da wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na haɗaka ba.
Okonkwo ya gargaɗi ADC kan zaɓen 2027
A wani labarin, kun ji cewa tsohon kakakin kamfen jam'iyyar LP a 2023, Kenneth Okonkwo ya shawarcu ADC ta yi taka-tsan-tsan wajen fidda ɗan takara a 2027.
Ya ce idan ADC ta ba ɗan Kudancin Najeriya takara tamkar ta matsa gefe ne, ta bai wa Shugaba Bola Tinubu damar tazarce a zaɓe mai zuwa.
Okonkwo ya ce matukar haɗakar ADC na don doke Tinubu, ya zama tilas ta ɗauko ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng

