Moro: Babban Sanatan PDP a Majalisa Ya Tsage Gaskiya kan Batun Shiga Hadaka
- Sanata mai wakiltar Benue ta Kudu a majalisar dattawa, Abba Moro, ya ba da tabbacin ci gaba da zama a jam'iyyar PDP
- Abba Moro ya bayyana cewa shi cikakken mamba ne a PDP kuma bai da wani shiri na ficewa daga jam'iyyar
- Sanatan ya kuma yi magana kan haɗakar jam'iyyun ƴan adawa inda ya ce ba zai shiga cikin tafiyar ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Sanata mai wakiltar Benue ta Kudu a majalisar dattawa, Abba Moro, ya bayyana cewa har yanzu shi cikakken mamba ne na jam'iyyar PDP.
Shugaban marasa rinjayen na majalisar dattawa ya kuma bayyana cewa bai da wani shiri na shiga haɗakar ƴan siyasa na jam'iyyun adawa.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata.
Sanata Abba Moro ya ce zama daram a PDP
Sanata Abba Moro ya ce yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP tun farkonta, kuma ya riƙe mukamai daban-daban na siyasa a ƙarƙashin jam’iyyar, don haka baya da niyyar ficewa daga cikinta.
"Ina so na bayyana sosai a nan cewa na shiga jam’iyyar PDP a shekarar 1998 lokacin da aka kafata, don haka ina ganin na cancanci na kira kaina ɗaya daga cikin masu kafa jam’iyyar."
"Ina ɗaya daga cikin mutanen farko da fara aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar nan."
- Sanata Abba Moro
Sanata Abba Moro ya ƙara da cewa bai taɓa barin PDP ba, kuma bai da wani shiri ko niyya na fita daga jam’iyyar.
“Ina son na jaddada cewa ban taɓa sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba. Ban taɓa shiga wata jam’iyya ba. Kuma har yanzu da nake magana da ku, ban sauya sheƙa ba."

Kara karanta wannan
Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai
"Ni cikakken mamba ne na jam’iyyar PDP. Ba zan shiga wata haɗaka ba. Ban shiga wata haɗaka ba. Kuma bana da niyyar shiga wani ƙawance."
- Sanata Abba Moro

Source: Twitter
Abba Moro ya ja kunnen ƴan haɗaka
Abba Moro ya gargaɗi masu shiga kawancen siyasa saboda fushi ko takaici, yana mai cewa Najeriya na buƙatar jagoranci mai zurfin tunani da kishin ƙasa.
Sanatan ya kuma shawarci ƴan siyasa da ƴan kasa gaba ɗaya da su yi amfani da tsarin da ake da shi a halin yanzu domin tsayawa takara a zaɓuɓɓuka.
Shugaban PDP ya aika da saƙon gargaɗi
A wani labarin kuma, kun ji cewa muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya aika da saƙon gargaɗi ga mambobin jam'iyyar.
Umar Damagum ya ja kunnen mambobin jam'iyyar da ka da su kuskura a same su da laifin cin amana ta hanyar haɗa kai da wasu jam'iyyun.
Shugaban na PDP ya bayyana cewa sun yi tanadi mai kyau na irin matakan ladabtarwa da za su ɗauka kan duk wanda aka samu da laifin cin amana.
Asali: Legit.ng
