'Gwamnoni da 'Yan APC na Goyon Bayan Hadakar ADC a Sirrance,' Babachir

'Gwamnoni da 'Yan APC na Goyon Bayan Hadakar ADC a Sirrance,' Babachir

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce wasu gwamnoni da manyan jiga-jigan APC na goyon bayan kawancen jam’iyyun adawa
  • Babachir Lawal ya bayyana cewa wasu daga cikin su ba su da ƙarfin hali su fito fili, amma suna goyon bayan canjin gwamnati a 2027
  • Dan siyasar ya zargi gwamnatin APC da rashin haɗin kai da tursasa ra’ayoyi, yana mai cewa gwamnatin Bola Tinubu ta gaza a fannoni da dama

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce wasu gwamnoni da manyan jam’iyyar APC na cikin masu marawa kawancen jam’iyyun adawa baya a ɓoye.

Babachir Lawal ya ce suna goyon bayan 'yan adawa ne domin fatan kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga Borno da karfinta, tana wawashe yan PDP da APC gabanin 2027

Babachir Lawal ce ya fita a APC ne saboda danniya
Babachir Lawal ce ya fita a APC ne saboda danniya. Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Lawal ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a TVC, inda ya ce da dama daga cikin su ba su da ƙarfin halin su fito fili, amma suna tare da burin samar da sabuwar gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wasu gwamnoni na tare da ADC" – Lawal

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Babachir Lawal ya ce 'yan adawa na samun goyon bayan wasu daga cikin APC a boye.

Babachir Lawal ya ce:

“Eh, akwai ’yan APC da ke tare da kawancen jam’iyyun adawa, kuma lokaci zai zo da za su bayyana kansu.
"Wasu ba su da ƙarfin hali kamar ni, amma suna nan—har da wasu gwamnoni a cikinsu"

Ya ce tun kafin ya fice daga APC a ranar 29 ga Yuni, ya riga ya fara aiki wa jam’iyyar adawa, kasancewar ya gaji da tsarin danniya da APC ke amfani da shi wajen murkushe mutane.

Kara karanta wannan

Babachir Lawal: Tsohon babban jami'i a gwamnatin Buhari ya fice daga APC

Lawal ya zargi APC da rashin haɗin kai, inda ya ce ko shawarwari ma ana ɗaukar su a matsayin cin amanar jam’iyya, lamarin da ya hana masu hangen nesa yin tasiri.

Tinubu ya ba abokansa kunya inji Babachir

Lawal ya ce mulkin shugaban kasa Bola Tinubu ya fusata da yawa daga cikin tsofaffin abokansa, dalilin da ya sa wasu ke kallon sauya gwamnati a matsayin mafita ga ƙasar.

Ya ce:

“Yawancinmu muna fatan samar da gwamnati mafi alheri, wacce za ta inganta rayuwar al’umma.
"Kuma babu laifi idan tsofaffin abokan Tinubu sun gaji da yadda yake tafiyar da mulki ko ya bar wasu su tafiyar da shi.”
Bababchir ya ce Tinubu bai kyauta wa wasu abokan shi ba
Bababchir ya ce Tinubu bai kyauta wa wasu abokan shi ba. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Babachir Lawal ya ce duk da sauya shekar gwamnoni zuwa APC, ba su da tasiri sosai a tsakanin talakawa saboda yawanci suna haka ne don tsare burinsu na gaba, ba don jama’a ba.

An yi taron ADC a jihar Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gamayyar jam'iyyun adawa sun yi taron kaddamar da ADC a jihar Gombe.

Manyan 'yan siyasa da suka hada da tsofaffin ministoci daga APC da PDP ne suka halarci taron hadakar.

Shugaban tafiyar, Sanata Muhammad Idris ya ce za su fadada jam'iyyar wajen bude kofar rajistar mambobi nan gaba kadan a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng