'Yan Arewa Sun Tunkari Tinubu, Sun Miƙa Sunan Wanda Suke So Ya Maye Gurbin Ganduje a APC
- Ƙungiyar magoya bayan APC a Arewacin Najeriya ta buƙaci Shugaba Tinubu ya amince Mohammed Kailani ya maye gurbin shugaban jam'iyya
- Shugaban ƙungiyar, Awwal Aliyu ya ce Mohammed jagora ne nagari, wanda zai iya dawo da martabar APC a idanun ƴan Najeriya
- Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Ƴan APC a Arewacin Najeriya sun fara maganar wanda ya kamata ya maye gurbin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje bayan ya yi murabus.
Wata ƙungiyar magoya bayan APC a Arewa ta bayyana goyon bayanta ga Mohammed Kailani domin ya zama sabon shugaban jam'iyya na ƙasa.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta rahoto cewa shugaban ƙungiyar, Awwal Aliyu ne ya bayyana hakan da yake hira da ƴan jarida a jihar Kadduna.

Kara karanta wannan
Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan dai na zuwa ne makonni bayan Ganduje ya yi murabus daga kujerar shugabancin APC bayan shafe watanni 22.
Ƴan Arewa sun goyi bayan Mohammed a APC
Awwal Aliyu, ya bayyana Mohammed Kailani a matsayin jagora nagari wanda zai iya dawo da haɗin kai da cigaba a jam’iyyar APC.
Ya ce shugabancin Kailani zai zama juyin juya hali ga jam’iyyar, yana mai ambato shekaru da dama da ya shafe yana nuna biyayya da kuma mu’amala da jama’a a matakin ƙasa da ƙasa.
“Nadin (Mohammed Kailani) zai farfado da jam’iyyar, ya dawo da amincin da aka rasa, kuma ya ƙarfafa haɗin kai a tsakanin shugabanni,” in ji Aliyu.
Ƴan APC sun faɗi alherin Mohammed Kailani
Ya ƙara da cewa ƙungiyarsu ta yaba da irin jajircewar Kailani ga jam’iyyar APC tun lokacin da aka kafa ta, yana mai cewa salon shugabancinsa na haɗin gwiwa ne kuma yana da tasiri.
A ruwayar Vanguard, Awwal Aliyu ya ce:
“Gogewar Mohammed da basirar da Allah ya ba shi ta shugabanci ba su da tsara. Ana girmama shi a fadin ƙasa sakamakon yadda yake haɗa kan mutane da kuma bai wa matasa dama.”

Source: Getty Images
Ƙungiyar APC ta aika saƙo ga Shugaba Tinubu
Awwal Aliyu ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da jagororin APC da su ba Kailani damar maye gurbin Ganduje, yana mai cewa hakan zai nuna cewa jam’iyyar na daraja cancanta, ƙwarewa da haɗin kai.
"Mohammad ya san irin ƙoƙarin da masu aikin sa kai ke yi kuma bai taɓa ja da baya wajen goyon bayansu ba. Shi mutum ne mai hangen nesa kuma yana da tarihin nasara,” in ji shi.
Hadimin Ganduje ya soki Shugaba Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce Shugaba Tinubu ya masu abubuwa mara daɗi.
Aminu Dahiru Ahmad ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ‘yan jam’iyyar APC da ke Kano rauni har sau uku.
A cewarsa, jam’iyyar APC ta samu karbuwa a wurin manyan ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyu a karkashin shugabancin Ganduje, ciki har dangwamnonin jihohi 2.
Asali: Legit.ng
