Shugaban PDP Ya Aika da Sabon Gargadi ga Mambobin Jam'iyyar
- Jam'iyyar PDP ta yi gargaɗi da babbar murya kan mambobinta masu yi mata zagon ƙasa da cin dunduniyarta
- Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa ya bayyana cewa ba za su lamunci ci gaba da cin amanar jam'iyyar ba
- Umar Damagum ya nuna cewa a shirye suke wajen hukunta duk wanda aka samu da laifin cin amanar PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta fitar da gargaɗi mai zafi ga mambobinta da ke shiga harkokin cin amanar jam’iyya da yi mata zagon ƙasa.
PDP ta bayyana cewa ba za ta yarda da rashin biyayya ko ɗabi’ar karya doka ba, musamman gabanin zaɓukan ƙananan hukumomi da ke tafe a babban birnin tarayya Abuja.

Source: Twitter
An bayyana wannan gargaɗi ne a ranar Talata yayin wani taron bayar da takardun shaidar tsayawa takara da aka gudanar a sakatariyar PDP ta Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wurin an taron, ƴan takara na zaɓukan ƙananan hukumomin sun karɓi takardunsu na shaidar samun takara a hukumance.
Wane gargaɗi shugaban PDP ya yi?
Yayin jawabi a madadin muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewa ta Tsakiya, Abdulrahman Mohammed, ya bayyana hukuncin da ke tafe ga mambobin da suka ci amanar jam’iyyar.
"Duk wani rashin ɗa’a ko hali na karya doka ba za a sake yarda da shi ba. Idan wani na ganin ba zai iya ɗaukar wannan nauyi ba, to ya janye nan take domin mu samu damar maye gurbinsa da wanda ya dace ba tare da ɓata lokaci ba."
- Umar Damagum
Damagum ya ƙara da cewa duk wani mamba da aka kama yana wasa da doka ko kuma yana haɗa kai da wasu jam’iyyu, za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.
"Yanzu muna da kwamitocin ladabtarwa masu aiki a matakin jiha da kuma ƙananan hukumomi. Duk wanda aka kama yana yin yaƙin neman zaɓe ko ƙulla alaka da wata jam’iyya, za a ɗauke shi da laifin cin amanar jam’iyya kuma za a hukunta shi."
- Umar Damagum

Source: Twitter
PDP ta shiryawa zaɓe
Game da shirin PDP kan zaɓen, Damagum ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta kare ƙuri'arta.
"Ba wanda zai yi wa zaɓenmu kutse. Da ikon Allah, za mu kasance a wuraren kaɗa ƙuri’a, mu tabbatar da an ƙirga ƙuri’un yadda ya kamata, sannan a sanar da waɗanda suka ci zaɓe da gaskiya."
- Umar Damagum
Tsohon shugaban PDP ya koma ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban PDP a jihar Katsina, ya fice daga jam'iyyar.
Honorabul Salisu Lawal Uli ya kuma koma jam'iyyar ADC ƙarƙashin tafiyar haɗakar ƴan adawa.
Tsohon shugaban na PDP ya bayyana cewa rikicin shugabancin da ya dabaibaye jam'iyyar, shi ne babban dalilin da ya sanya ya tattara ƴan komatsansa ya fice.
Asali: Legit.ng
