Tsohon na Kusa da Atiku Ya Yi Masa Wankin Babban Bargo kan Takarar Shugaban Kasa

Tsohon na Kusa da Atiku Ya Yi Masa Wankin Babban Bargo kan Takarar Shugaban Kasa

  • Segun Sowunmi ya yi wasu kalamai na suka kan tsohon ubangidansa, a siyasance, Alhaji Atiku Abubakar
  • Tsohon mai magana da yawun bakin kamfen ɗin Atiku na 2023, ya soke shi kan ci gaba da neman takarar shugaban ƙasa da yake yi
  • Ya bayyana cewa lokaci ya yi da tsofaffi irinsu Atiku za su kauce domin ba sabon jini damar jan ragamar ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Ogun, Segun Sowunmi, ya soki tsohon ubangidansa, Alhaji Atiku Abubakar.

Segun Sowunmi ya soki Atiku Abubakar ne saboda ci gaba da neman kujerar shugaban ƙasa tun daga shekarar 1992.

Sowunmi ya caccaki Atiku Abubakar
Segun Sowunmi ya caccaki Atiku Abubakar Hoto: Segun Sowunmi
Source: Twitter

Segun Sowunmi ya bayyana hakan ne a cikin shirin 'LunchTime Politics' na tashar Channels Tv a ranar Talata, 8 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Segun Sowunmi ya ce kan Atiku?

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya fadi damar da Atiku ya rasa ta zama shugaban kasa

Ya zargi Atiku da tada zaune tsaye a ƙasar nan ta hanyar siyasar da yake yi domin cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.

A cewarsa, duk da irin tsawon lokacin da Atiku ya kwashe yana fafutukar zama shugaban ƙasa, bai taɓa bayyana wani ingantaccen ra’ayi ko tsari da zai kawo ci gaba ga ƙasar nan ba.

Ya ƙara da cewa kujerar shugaban ƙasa ba gadon Atiku ba ce, yana mai cewa lokaci ya yi da za a yi watsi da ƴan siyasar da suka dade a fagen siyasar Najeriya tun daga shekarar 1992.

"Ta hanyar irin siyasar da kake yi, kana dagula tsarin ƙasa, kana tada hankalin jama’a, har ma ba ka barin waɗanda ke gudanar da mulki kullum su samu natsuwa da kwanciyar hankali domin gudanar da ayyukansu."
"Kuma ba mu ji wani abu daga gare ka ba da zai zaburar da mu har mu ce lallai kana da wani abu na musamman."
“Me kake kawowa? Ba mu gwada ka ba a baya? Ba mu ba ka dama a baya ba? Ba ka bin mu bashin shugabancin Najeriya."

Kara karanta wannan

"Zai iya kifar da Tinubu," Momodu ya faɗi wanda ya dace ADC ta tsayar takara a 2027

"Kuma idan har za mu koma Arewacin Najeriya a 2027, ya fi dacewa ka nemo mana wani matashi daga Arewa, wanda ya fi ƙwazo da basira. Mu ce mun gama da mutanen da suka fara siyasa tun shekarar 1992."

- Segun Sowunmi

Segun Sowunmi ya yi kalamai kan Atiku
Sowunmi ya bukaci Atiku ya koma gefe Hoto: Segun Sowunmi
Source: Facebook

Sowunmi ya soki ƴan haɗaka

Sowunmi ya kuma soki shugabannin haɗakar ƴan adawa, yana mai cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, shi ne kaɗai ɗan siyasar da ke ba ƙungiyar kuzari.

Ya bayyana cewa, da Peter Obi bai yi abin a zo a gani ba a zaɓen da ya gabata, da babu wani dalili da za a kafa wannan haɗakar.

Hadimin Tinubu ya soki Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin Shugaba Bola Tinubu ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Daniel Bwala ya bayyana cewa da wuya Atiku Abubakar ya taɓa zama shugaban ƙasan Najeriya a rayuwarsa.

Hadimin na Tinubu ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya rasa damar da ya samu ta zama shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng