"Zai Iya Kifar da Tinubu," Momodu Ya Faɗi Wanda Ya Dace ADC Ta Tsayar Takara a 2027
- Tsohon jigon PDP, Dele Momodu ya ce Atiku Abubakar ne ya fi dacewa haɗakar ƴan adawa ta tsayar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027
- Fitaccen ɗan jaridar ya bayyana cewa Atiku ya fi sauran masu neman tikitin jam'iyyar haɗaka ƙarfin da zai gwabza da Shugaba Bola Tinubu
- Momodu, wanda ya taɓa neman tikitin takarar shugaban ƙasa ya roki magoya bayan Obi da Amaechi, su goyi bayan ɗan takararsu cikin lumana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Fitaccen ɗan jarida kuma mai mujallar Ovation, Cif Dele Momodu, ya bayyana tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin zabinsa a 2027.
Momodu ya ce Atiku Abubakar ne wanda ya fi cancanta haɗakar jam'iyyun adawa karkashin inuwar ADC ta bai wa tikitin takarar shugaban kasa a zaɓe mai zuwa.

Source: Facebook
Tsohon jigo a PDP ya faɗi haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Siyasa a Yau na Channels TV.

Kara karanta wannan
Lukman ya rabawa Atiku da Obi gardama, ya faɗi wanda ADC za ta tsayar takara a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dele Momodu ya ce Atiku ne zaɓinsa a ADC
Momodu ya jaddada cewa duk da alaƙar abota da ke tsakaninsa da ɗan takarar LP a 2023, Peter Obi, hankalinsa ya fi kwanciya idan aka tsayar da Atiku.
A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban ƙasar shi ne madugun adawa, wanda ke da ƙarfin da zai ragargaji APC a zaɓen 2027 daga cikin masu neman takara a ADC.
“Zaɓi na shi ne Atiku, amma ina tsammanin ‘yan Obidients za su ɗauki Peter Obi, haka masu goyon bayan Amaechi za su ɗauki na su.
"Siyasa lissafi ce, mafi yawan waɗanda suka fi ɗaukar zafi kan halin da wannan gwamnatin ta jefa kasar nan a yau suna Arewacin Najeriya.”
- Dele Momodu.
Momodu, wanda tsohon jigo ne a PDP da yanzu ya koma cikin ADC, ya bayyana cewa wannan shi ne ra'ayinsa da zaɓinsa amma ba dole ba ne ya yi daidai da na wasu.
Momodu ya buƙaci ADC ya shirya zaɓe mai tsafta
Sai dai ya yi kira da a shirya zabe fidda gwani mai tsafta da gaskiya don fitar da ɗan takarar ƙawancen ƴan adawa, wanda zai iya gwabzawa da Shugaba Tinubu, Tribune Online ta rahoto.
Ya kuma zargi APC da ƙoƙarin cusawa ADC ɗan takara daga Kudu, yana zargin cewa APC tana tsoron ƙarfin Atiku, don haka take yunkurin bata masa suna.
“Idan ka saurari Wike da kyau, su ke ta yaɗa cewa shugaban ƙasa na gaba dole ne ya fito daga Kudancin Najeriya.
"Amma sun san babu ɗan Kudu da ke da ƙarfi da tasiri a ƙasa gaba ɗaya. Da Wike yana daga cikin masu neman takara, amma yanzu yana marawa Asiwaju baya,” in ji Momodu.

Source: Facebook
Momodu ya yi kira ga magoya bayan duka masu neman tikitin takarar jam'iyyar haɗaka watau ADC su goyi bayan duk wanda suke so cikin lumana, sannan su amince da duk wanda ya samu nasara a zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai
Wani ɗan amutun Atiku, Kabir Dogo ya shaida wa Legit Hausa cewa suna nan tare da tsohon mataimakin shugaban ƙasa duk inda ya shiga.
A cewarsa, babu wani ɗan takara a jam'iyyar haɗaka da zai iya cin galaba kan APC da ya wuce Alhaji Atiku Abubakar.
"Muna kira ga shugabannin jam'iyyarmu mai albarka watau ADC su ba Atiku takara, shi ne kaɗai mafita, wanda zai iya share hawayen ƴan Najeriya," in ji shi.
Jiga-jigai na tururuwar shiga ADC a Borno
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC wacce haɗakar ƴan adawar Najeriya sika zaɓa ta ƙara karfi a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana samun sauya sheƙa mai yawa daga wasu jiga-jigan jam’iyyu ciki har da APC zuwa ADC.
Alhaji Idris Mamman Durkwa, tsohon mai neman takarar gwamna jihar Borno ns cikin waɗanda suka sauya sheka zuwa ADC.
Asali: Legit.ng
