ADC: Atiku Ya Fara Kokarin Jawo Jagororin zuwa Tafiyar Fatattakar APC a 2027

ADC: Atiku Ya Fara Kokarin Jawo Jagororin zuwa Tafiyar Fatattakar APC a 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kira ‘yan PDP da su shigo hadakar adawa domin ceto Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan an samu amincewa da a hadu a jam'iyyar adawa ta ADC domin fafutukar kwato mulki a 2025
  • Ana sa ran za a tabbatar da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin gamayyar adawa bayan taron ranar Laraba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga shugabannin PDP da su hada kai da sauran jam’iyyun adawa domin ceto Najeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran 'yan adawa za su kammala shirin amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandamalin gamayyar adawa.

Jagororin adawa sun hadu a ADC
Atiku na kokarin jawo manyan PDP zuwa ADC Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023 a PDP, ya jagoranci wani muhimmin taro da magoya bayansa a ranar Talata a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani mai zafi bayan Atiku, El Rufa'i da Peter Obi sun yi hadaka a ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC: Atiku ya jagoranci taro a Abuja

Trust Radio ta wallafa cewa taron ya mayar da hankali ne wajen hada kan ‘yan siyasa masu ra’ayi daya, da sake fasalin jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027.

Wani jigo daga cikin kawancen, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa za a tabbatar da amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandamalin adawa a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa sakamakon taron na Laraba zai danganta da ra’ayoyin da aka samu daga tuntubar jiga-jigai da aka yi a makon da ya gabata.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
Atiku ya ce akwai bukatar a ceto Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya ce:

“Shugabanni da dama sun bukaci lokaci domin tuntubar magoya bayansu kan batun shiga ADC."
"Taron Laraba zai kasance na tattara ra’ayoyin da kuma amincewa da su. Saboda haka, muna sa ran samun matsaya ta karshe.”

Atiku, ‘yan adawa sun cimma matsaya

Bayan kammala taron, tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, ya bayyana cewa ana kokarin samar da matsaya ta bai daya domin ceto tsarin dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

2027: Atiku, Sule Lamido da jiga jigan PDP sun shiga ganawar gaggawa a Abuja

Sanarwar ta bukaci dukkan mambobin PDP masu kishin kasa da sauran ‘yan Najeriya masu gaskiya da rikon amana da su shiga cikin kawancen don ceton kasa.

Daga cikin manyan ‘yan siyasa da suka halarci taron har da tsohon kakakin majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

Haka kuma, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, da wasu tsofaffin gwamnoni da dama sun kasance cikin mahalarta taron.

ADC: An yi martani kan hadakar adawa

A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar APC mai mulki ta yi martani kan yadda manyan 'yan adawa a kasar nan suka hada kansu a jam'iyyar ADC.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa sabon kawancen da ake ƙulla wa a Abuja, ba zai iya kifar da gwamnatin APC ba.

Shugabannin sabuwar kawancen adawa sun amince su yi amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin da za su fuskanci APC a zabe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng