Cire Tallafi: Gaskiya Ta Fito kan Zargin Buhari da Neman Haɗa Ƴan Najeriya Faɗa da Tinubu
- Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana gaskiya kan zargin da ake yi wa gwamnatin da ta shude
- Malam Garba Shehu ya ce Buhari bai yi wani shiri na kawo cikas ga gwamnatin Bola Tinubu ba musamman kan cire tallafin mai
- Ya ce dukkansu 'yan jam'iyyar APC ne, don haka babu yadda Buhari zai hana Tinubu nasara ko ya jefa shi cikin matsala
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana kan mai gidansa.
Malam Garba Shehu, ya ce Buhari bai taba shirin kawo cikas ga gwamnatin Bola Tinubu ba musamman a zaben 2023.

Source: Facebook
Hadimin Buhari ya kare shi kan cire tallafi
Garba Shehu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin tattaunawa da manema labarai gabanin kaddamar da littafinsa ranar 9 ga watan Yuli, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
"Ba dan Allah ba ne," An gano abin da ke tilastawa gwamnonin PDP sauya sheƙa zuwa APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai rade-radin cewa Buhari ya jinkirta cire tallafin mai har sai a karshe domin ya jefa sabuwar gwamnati cikin tsangwama da bacin rai.
Mutane na korafi game da wahalhalu tun bayan cire tallafin mai da Tinubu ya sanar a jawabin rantsuwarsa.
Amma Garba Shehu ya ce wadannan rade-radin ba daidai ba ne, yana mai cewa ba a tsara cire tallafin ne don cutar da gwamnatin Tinubu ba.
Garba Shehu ya jaddada alaƙar Buhari da Tinubu
Garba Shehu ya jaddada cewa Buhari da Tinubu dukkansu ‘yan jam’iyyar APC ne, don haka babu dalilin su cutar da juna a cikin mulki.
Ya ce:
“A matsayinsu na mambobin APC, ba za su taba yin shiri na bata gwamnatin da kansu ba."
Garba Shehu ya ce Buhari ya zo da gaskiya kuma ya bar gwamnati da mutuncinsa, ya ce tarihi zai yabi Buhari bisa ayyukansa.
“Shugaba Buhari ba dan jan riya ba ne. Ayyukansa ne kawai ya so su taimaka wa talakawa."

Kara karanta wannan
Maryam Shetty ta tofa albarkacin bakinta kan murabus ɗin Ganduje daga shugabancin APC
- Cewar Garba Shehu

Source: Facebook
Garba Shehu ya magantu kan alaƙarsa da Atiku
Garba Shehu ya ce bai yi kuskure ba da ya bar Atiku Abubakar domin ya yi aiki da Buhari a lokacin mulkinsa.
Yayin da yake amsa tambaya kan yadda yake sukar Atiku, Shehu ya ce to me ya sa ba zai soki Atiku ba in yana tare da Buhari?
Ya ce da har yana yi wa Atiku shishshigi a boye, to Buhari da kansa ba zai yarda da shi ya cigaba da aiki a fadar gwamnati ba.
Garba Shehu ya kasance kakakin Atiku kafin daga baya ya koma aiki da shugaba Muhammadu Buhari a gwamnatin APC.
Tinubu ya yabawa Buhari a ranar dimukraɗiyya
Kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tuna da Muhammadu Buhari a jawabinsa na ranar dimokuradiyya a zauren Majalisar Tarayya.
Shugaba Tinubu ya yabawa Buhari bisa matakin da ya ɗauka na ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar dimokuraɗiyya a Najeriya.
Bola Tinubu ya sha alwashin cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen kare tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng