Atiku Ya Taɓo Batun Ritaya a Siyasa, Ya Faɗi Abin da Zai Maida Hankali bayan Barinta

Atiku Ya Taɓo Batun Ritaya a Siyasa, Ya Faɗi Abin da Zai Maida Hankali bayan Barinta

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana abin da zai yi bayan ya bar siyasa a rayuwarsa
  • Atiku ya ce zai koma jami’a bayan ritaya daga siyasa, yana mai bayyana sha’awarsa ga ilimi da haɓaka ɗan Adam
  • Ya bayyana haka ne yayin bikin yaye ɗalibai a makarantar Pacesetters Abuja, inda ya jaddada cewa ilimi mabuɗin ci gaban ƙasa ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Abubakar Atiku ya tabo batun ritaya a siyasa da kuma abin da zai yi.

Atiku ya bayyana cewa zai koma jami’a bayan ya yi ritaya daga siyasa, yana nuna sha'awarsa ga ilimi da ci gaba.

Atiku ya yi magana kan ritaya a siyasar Najeriya
Atiku ya fadi abin da zai yi bayan ritaya a siyasa. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Getty Images

Abin da Atiku ya ke sha'awa bayan barin siyasa

Atiku, wanda shi ne wanda ya kafa American University of Nigeria (AUN), ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin bikin yaye ɗaliban a Abuja, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Abin da ƴan Najeriya ke cewa da Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya tuna yadda sha'awarsa ga ilimi ta kai shi ga kafa makarantar yara, sakandare, daga baya kuma jami’a.

Ya jinjina wa wanda ya kafa Pacesetters Schools Abuja, Barrister Kenneth Imansuangbon, bisa jajircewarsa wajen gina makarantu masu inganci a Najeriya.

Atiku ya bayyana ilimi a matsayin “mabuɗin” da zai buɗe ƙofofin ci gaban Najeriya da kuma ciyar da ƙasa gaba a ɓangaren tattalin arziki.

Ya jaddada cewa ilimi yana da matuƙar muhimmanci ga haɗin kan ƙasa, kwanciyar hankali da ci gaba, musamman don hana rarrabuwar kawuna.

Atiku zai koma makaranta bayan barin siyasa
Atiku ya nuna sha'awar komawa jami'a bayan ritaya a siyasa. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Depositphotos

Atiku ya bayyana muhimmancin ilimi a rayuwa

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ya ce kuɗaɗe da sabon kundin karatu mai jaddada sana’o’i suna da matuƙar muhimmanci.

Atiku ya bayyana rawar da ilimi ya taka a rayuwarsa, yana cewa:

“Ilimi shi ya mayar da ni a yadda kuke ganina yau, ina taya abokina ( Kenneth Imansuangbon) murna bisa saka jari a ci gaban ɗan Adam, babu mafi alheri da ya wuce ilimi.

Kara karanta wannan

"Bai taba ba": Tsohon hadimin Tinubu ya yi fallasa kan shugaban kasa

“Ilimi yana baiwa mutum damar zama likita, injiniya ko duk wata sana’a da yake so, ina taya ɗalibai murna, kuma na yi farin ciki da ganin wasu daga cikin dalibai na a cikin su.
“Ina gode wa Shugaban makaranta da ya gayyace ni wannan rana mai tarihi, wadda ta dace da sha'awata ga ilimi."

Ya ce hakan ya yi tasiri a iliminsa, kuma hakan ne ya sa ya ɗauki tsarin karatun Amurka a makarantun da ya kafa a Najeriya, cewar The Nation.

Atiku ya gana da yan siyasa a Abuja

Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa an kusa kaddamar da wani babban kawance na ‘yan adawa domin farfaɗo da Najeriya.

Wani gungun masu ruwa da tsaki daga Arewa maso Yamma sun shaida masa cewa suna shirye-shiryen goyon bayan wannan kawance a zaben 2027.

Atiku ya jaddada cewa Najeriya na bukatar canji mai ma’ana, kuma wannan ƙawance na da ƙwarewar da za zai iya fuskantar matsalolin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.