'Murabus Ɗin Ya Fi Masa Alheri': Jigon APC Ya Faɗi Wulaƙanci da Aka Shiryawa Ganduje
- Wani jigo a APC daga Kano ya ce murabus da Abdullahi Ganduje ya yi dabara ce don kauce wa kaskanci da saukar da shi da karfi
- Jigon ya bayyana cewa akwai shiri a asirce na fatattakar Ganduje idan har bai bi umarnin fadar shugaban kasa ba
- Ya kuma ce Ganduje ya taimaka wajen karfafa APC da jawo ‘yan siyasa da dama, don haka dole a girmama gudunmawarsa ga jam’iyyar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani jigo a jam’iyyar APC a Kano, Alhaji Alhassan Yaryasa ya yi magana bayan Abdullahi Ganduje ya yi murabus.
Yaryada ya bayyana murabus da Ganduje ya yi daga shugabancin jam’iyyar a matsayin dabara mai amfani.

Source: Twitter
Yaryasa ya bayyana hakan ne cikin wata hira ta waya da wakilin Punch a Kano a ranar Lahadi 29 ga watan Yunin 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya fadi dalilin yin murabus
Hakan ya biyo bayan murabus da tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yi a ranar Juma'a 27 ga watan Yunin 2025.
An yi ta yaɗa jita-jita kan dalilin murabus din na shi yayin da wasu ke ganin rigimar cikin gida ne ta jawo haka.
Sai dai Ganduje a cikin wasikar ajiye aiki, ya bayyana cewa murabus din na da nasaba da kula lafiyarsa a yanzu.
Jigon APC zargin neman ciwa Ganduje mutunci
Jigon jam'iyya mai adawa a Kano ya ce akwai alamun za a tilasta masa murabus ko da bai yi niyya ba.
Ya zargi cewa an shirya wata makarkashiya da za ta kunyata Ganduje daga mukaminsa idan har ya ki yarda da abin da fadar shugaban kasa ke so.
Ya ce:
“Mun san akwai shirin kawo Sanata Rabi’u Kwankwaso cikin APC don ya zama mataimakin Tinubu a 2027. Murabus da Ganduje ya yi, shine mafita."

Kara karanta wannan
Ana tsaka da maganar Ganduje, an yaɗa murabus ɗin sakataren gwamnati, gaskiya ta fito

Source: Facebook
An yabawa Ganduje bayan ya yi murabus
Yaryasa, wanda ya taba zama mai jagorantar kamfen din Tinubu a Kano ta Kudu, ya ce Ganduje ya cancanci yabo da girmamawa saboda rawar da ya taka.
“Kar ku manta Ganduje ya shigo da manyan ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyu zuwa APC, ciki har da sanata da ‘yan majalisa.
“Don haka, ya fi dacewa ya sauka da mutunci kafin su tilasta masa ya sauka cikin kaskanci."
- Cewar Yaryasa
Game da ko ya dace shugaban jam’iyyar na kasa ya fito daga yankin Arewa maso Yamma, Yaryasa ya ce a bi tsarin adalci da gaskiya.
Ya kara da cewa:
“Ko wane yanki ne ya dace ya ba da shugaban jam’iyya, a bar shi. Hakan zai tabbatar da adalci da daidaito."
An fadi babban dalilin murabus din Ganduje
A baya, kun ji cewa ana ta hasashe kan dalilin murabus din Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC mai mulki a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan
Bayan hasashe da dama, an gano 'dalilin' murabus din Ganduje daga shugabancin APC
Wasu sun yi zargin cewa DSS na tuhumarsa da cin hanci, musamman kan zaben Bwari da aka ce an sauya sakamako.
Sannan an ce Bola Tinubu ne ya umarci gwamnonin APC da su “ba da shawara” ga Ganduje ya sauka bayan rahoton DSS.
Asali: Legit.ng
