'Lamiɗo Ya Yi Masa Ƙarya: An Faɗi Yadda Tinubu Ya Fashe da Kuka kan Zaɓe a Amurka
- Dan gwagwarmaya, Jumoke Ogunkeyede ya bayyana yadda Bola Tinubu ya shiga damuwa a lokacin rigimar zaben 1993 saboda aka soke
- Ogunkeyede ya ce Tinubu ya taba kuka a Amurka saboda rabuwar kawuna tsakanin 'yan gwagwarmayar ranar 12 ga watan Yuni
- Ya karyata zargin Sule Lamido da ke cewa Tinubu bai goyi bayan gwagwarmaya ba har sai bayan Abacha ya hau mulki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Jagoranci ƙungiyar NADECO, Jumoke Ogunkeyede daga Amurka ya yi magana kan rawar da Bola Tinubu ya taka a zaben 1993.
Ogunkeyede wanda yanzu ya dawo gida, ya ba da labarin abubuwan da suka faru a yakin neman zaben June 12 a lokacin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida.

Source: Twitter
Yadda Tinubu ya yi gwagwarmaya a 1993
Dan gwagwarmayar ya bayyana hakan ne a cikin wata hira a Channels TV, yana jinjinawa kokarin Tinubu wajen hada kai tsakanin bangarorin gwagwarmayar a ketare.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da maganar Ganduje, an yaɗa murabus ɗin sakataren gwamnati, gaskiya ta fito
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ogunkeyede, shugaban 'United Committee to Save Nigeria a New York' bayan soke zaben 1993, ya ce Tinubu ya taba kuka saboda rabuwar kungiyoyin.
Game da zargin Lamido cewa Tinubu bai shiga gwagwarmaya ba sai bayan Abacha ya hau mulki, Ogunkeyede ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
Ogunkeyede ya ce:
"Ina bakin ciki da cewa watakila yana cikin maye. Shugaba Tinubu ya tsaya tsayin daka don kare gaskiya.
"Lokacin da muke cin abinci da Cif Enahoro, Tinubu ya kusa yin kuka, yana cewa lallai dole a kammala wannan gwagwarmaya."

Source: Facebook
June 12: Gudunmawar da Tinubu ya bayar
Ogunkeyede ya ce Tinubu ya umarce shi da ya hada 'yan gwagwarmaya da ke ketare don hada kai da ceto Najeriya daga rugujewa.
Ya ce:
"Na ga Tinubu ya fara kuka a New York yana sanye da riga ruwan kasa, yana cewa mu daina sabani, mu hada kai.
"Na marabce shi a New York. Mutanen da suka halarci wannan taron za su iya tabbatar da abin da na fada.
"Tinubu ya yi aiki tukuru don kare Najeriya daga rugujewa, kuma muna godiya da shi yanzu shugaban kasa ne."
An bukaci hadin kai domin gina Najeriya
Ogunkeyede ya ce ana bukatar a hada kai don tabbatar da ci gaban Najeriya da fatan Najeriya za ta tsira.
Kan jerin sunayen wadanda aka girmama ranar June 12, dan gwagwarmaya ya ce an manta da su da suka sadaukar da rayukansu da dukiyoyi.
Ya ce ya kasance cikin mutum goma na farko, wasu da dama kamar su Janar Akinrinade sun bar gidajensu saboda gwagwarmaya.
Yadda mahaifiyar Tinubu ta gagari Abacha
A baya, kun ji cewa dan marigayi MKO Abiola ya yi magana kan mulkin marigayi Janar Sani Abacha da rigimar zaben 12 ga watan Yunin 1993.
Jamiu Abiola ya ce Abacha ya gagara kashe mahaifiyar Bola Tinubu, Alhaja Abibatu Mogaji, saboda girmamawa da karbuwarta a idon jama'a.
Ya ce Alhaja Mogaji ta yi adawa da soke zaben 1993, har ta cire mayafinta tana rokon Ibrahim Babangida ya soke matakin da ya dauka.
Asali: Legit.ng
