Ana Zargin an Taso na Kusa da Tinubu Ya Yi Murabus domin Karɓar Kujerar Ganduje
- Ana cigaba da samun bayanai bayan tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam'iyyar
- An ce ana matsin lamba ga George Akume ya yi murabus don ya karɓi shugabancin jam’iyyar
- Jihohin Arewa ta Tsakiya sun sake neman kujerar shugaban jam’iyya, suna ganin Akume ya fi cancanta bisa kwarewarsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Bayan murabus ɗin Dr. Abdullahi Ganduje daga matsayin Shugaban Jam’iyyar APC, an taso sakataren gwamnatin tarayya.
Majiyoyi sun ce ana matsin lamba ga Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume ya ajiye aikinsa domin karɓar mukamin.

Source: Facebook
Zargin taso Akume a gaban kan kujerar Ganduje
Rahoton Thisday ta gano cewa matsin lamba ga tsohon gwamnan jihar Benue ya biyo bayan sabuwar kiran da jiga-jigan APC daga yankin Arewa ta Tsakiya ke yi.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da maganar Ganduje, an yaɗa murabus ɗin sakataren gwamnati, gaskiya ta fito
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan yankin yana ganin lokacinsu ne domin samun kujerar bayan Ganduje ya ajiye aiki a ranar Juma'a.
Murabus ɗin Ganduje ya haifar da sabon kira daga shugabannin jam’iyya daga yankin Arewa ta Tsakiya.
Hakan bai rasa nasaba da kokarin dawo da kujerar ga yankin, bisa tsarin raba madafun iko da aka tsara a shekarar 2022.
Jiga-jigan yankin na ganin cewa, da kwarewar Akume da tarihin aikinsa, shi ne mutum mafi dacewa da wannan matsayi.
A baya dai tsohon gwamnan jihar Kano ya karɓi kujerar ne a watan Agustan 2023 bayan murabus ɗin Sanata Abdullahi Adamu, wanda ya fito daga Arewa ta Tsakiya.

Source: Facebook
An nada shugaban riko na APC
An ba shugaban Jam’iyya na Arewa, Hon. Ali Dalori ya karɓi ragamar mulki a matsayin mukaddashi, kamar yadda kundin tsarin mulki na jam’iyyar ya tanada.
Dalori zai riƙe kujerar ne har zuwa watan Disamba lokacin da za a nada sabon shugaba na dindindin ta hanyar taron kwamitin NEC na jam’iyyar, cewar Arise News.

Kara karanta wannan
Bayan hasashe da dama, an gano 'dalilin' murabus din Ganduje daga shugabancin APC
A baya, ko da wasu ƙungiyoyi daga Arewa ta Tsakiya sun nuna adawa da nadin Ganduje, taron NEC da aka yi a watan Fabrairu ya tabbatar da nadin da kuma daidaita kujerar shugaba da yankin Arewa maso Yamma.
Yanzu da Abdullahi Ganduje ya sauka, wasu shugabannin jam’iyyar daga Arewa ta Tsakiya sun dawo da kokarinsu na ganin yankin ya samu kujerar shugabanci.
Ko da yake Akume bai bayyana sha’awarsa ta zama shugaban jam’iyyar ba, an gano cewa akwai akalla mutane biyar daga yankin da ake hasashen suna sha’awar mukamin.
Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Umar Tanko Al-Makura; tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye; tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Sai kuma Sanata Solomon Ewuga, da Sanata Sani Musa, wanda ke wakiltar yankin Neja Gabas a majalisar dattawa.
An musanta labarin murabus din Akume
Kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta yi magana kan jita-jitar cewa an sauya Sanata George Akume daga mukaminsa na sakataren gwamnatin tarayya.
Mai ba shugaban kasa shawara kan bayanai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa "babu wani sauyi" game da matsayin Akume, kuma ya ce Bola Tinubu bai nada wani ba.
Fadar ta ce masu yada jita-jita na kokarin tada zaune tsaye, ta kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da labaran bogi da ba su da tushe.
Asali: Legit.ng