Zaɓen 2027: Dalilai 3 da Za Su Sanya Atiku Ya Kayar da Tinubu idan Ya Samu Tikiti
- Akwai yiwuwar Atiku Abubakar ya samu tikitin takarar shugaban kasa a 2027 karkashin jam'iyyar haɗaka da 'yan adawa ke son kafawa
- A watan Afrilu 2025, Atiku ya bayyana cewa haɗakar 'yan adawa ce kawai za ta iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
- A cikin wannan rahoto, Legit Hausa ta kawo wasu muhimman dalilai uku da za su sanya Atiku ya doke Tinubu idan ya samu tikitin takara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Yayin da siyasar zaben 2027 da ke tafe take ƙara daukar zafi, ƴan siyasa suna shiri don karɓa ko riƙe mulki.
A cikin wannan yanayin, babban tambayar da ke bakin yawancin ƴan Najeriya ita ce, shin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai iya doke Shugaba Bola Tinubu don zama shugaban Najeriya?

Source: Facebook
2027: Atiku ya hada kan 'yan adawa
Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2019 da 2023, amma ya fara neman kafa jam'iyyar haɗakar 'yan adawa don kalubalantar APC a 2027.
Wannan haɗakar ta haɗa da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP Peter Obi, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, da kuma tsohon shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), Akin Ricketts.
Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, ya tuntuɓi manyan ƴan siyasa daga jam'iyyu daban-daban.
2027: Dalilai 3 da za su sa Tinubu ya sha kasa
A cikin wannan rahoton, jaridar Legit.ng ta dubi mahimman abubuwa guda uku da za su iya taimaka wa Atiku ya doke Tinubu idan har ya zama ɗan takarar jam'iyyar ƙawancen.
1. Goyon bayan jama'a daban-daban:
Atiku Abubakar, wanda ɗan asalin jihar Adamawa ne, yana da goyon bayan al'umma da suka fito daga kaliba da addini daban daban.
Yana da abokan arziki daga ko'ina a faɗin Najeriya. Wasu masu ruwa da tsaki a siyasa suna goyon bayan Atiku sosai saboda jajircewarsa a al'amuran da suka shafi buƙatun ƙasa.
2. Atiku a matsayin 'mai haɗa kan al'umma':
Magoya bayansa suna yi wa Atiku laƙabi da 'mai haɗa kan al'umma', suna masu cewa an samo laƙabin ne sakamakon kokarinsa na hada kan manyan kasa don ci gaban jama'a.
Atiku ya goyi bayan waɗanda suke zargin ana so a fifita wani yanki kan wani kuma ya yi alƙawari a wurare da dama cewa zai haɗa kan Najeriya idan aka zaɓe shi matsayin shugaban ƙasa.

Source: UGC
3. Bacin rai na jama'a:
Yawancin ƴan Najeriya suna ganin cewa babu wani ci gaban azo a gani a tattalin arziki da aka samu tun lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki a watan Mayu 2023; don haka, ba za su damu da canjin shugabanci ba.
A cikin shekarar da ta gabata, hauhawar farashin kayayyaki ya jawo tsadar farashin abinci, lamarin da ya sa mutane da yawa ke samun wahalar cin abinci sau uku a rana.

Kara karanta wannan
Dalla dalla: Abubuwan da ake buƙata wajen kafa sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya
A hannu daya, samar da abinci a cikin gida ya ragu, galibi saboda manoma a yankunan Arewacin ƙasar da ke samar da abinci suna fuskantar hare-hare daga ƴan ta'adda kamar Boko Haram da sauran ƴan bindiga.
Tinubu ya yi magana kan Atiku, El-Rufai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ShugabaBola Ahmed Tinubu ya bayyana haɗakar ƴan adawa da ke shirin kayar da shi a 2027 a matsayin ƴan gudun hijirar siyasa.
Bola Tinubu ya buƙaci magoya bayansu su yi fatali da su, kada su tsaya ɗaga hankalinsu kan haɗakar wacce Atiku Abubakar ke jagoranta.
Har ila yau, shugaban ƙasa ya kare kansa daga zargin fara yaƙin neman zaɓe tun kafin hukumar INEC ta bayar da damar hakan.
Asali: Legit.ng

