Bayan Ganduje, Hadimin Shugaban PDP Na Kasa Ya Yi Murabus
- Hadimin muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum ya yi murabus daga kan muƙaminsa
- Malam Abubakar Yusuf Dingyadi wanda ke ba Damagum shawara kan harkokokin yaɗa labarai ya ajiye aikinsa
- Tsohon hadimin na Damagum ya kasance gogaggen ɗan jarida wanda ya daɗe yana taka muhimmiyar rawa a PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum, ya rasa ɗaya daga cikin hadimansa.
Babban mai ba Umar Iliya Damagum shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Malam Yusuf Abubakar Dingyadi, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da ya rubuta a ranar 25 ga watan Yuni, 2025, wacce ya aika wa muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa hadimin shugaban PDP ya yi murabus?
Malam Abubakar Yusuf Dingyadi ya bayyana godiyarsa ta musamman bisa damar da aka bashi na yi wa jam’iyyar hidima, ko da yake bai bayyana dalilin ajiye aikinsa ba.
“Duk da cewa na yaba da goyon baya da addu’o’in mambobin jam’iyyar PDP a lokacin da nake kan wannan muƙami, ina mai ƙara godiya da duk gudunmawar da aka bani domin nasarar aikin da aka ɗora min."
- Malam Abubakar Yusif Dingyadi
Wane Abubakar Yusuf Dingyadi?
Malam Abubakar Yusuf Dingyadi ya shahara a matsayin tushe mai inganci wajen yaɗa sahihan bayanai kan al’amuran jam’iyyar PDP, musamman a lokutan rikicin cikin gida na jam’iyyar.
Fiye da shekara uku, ya kasance murya mai karfi wajen kare muradun jam’iyyar da kuma inganta haɗin kai ta kafafen yaɗa labarai daban-daban, ciki har da rediyo, talabijin da jaridu.
A matsayinsa na gogaggen masani kan harkokin siyasa da yaɗa labarai, Dingyadi ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP tun lokacin mulkin Obasanjo/Atiku, kuma ya taɓa aiki a ƙarƙashin tsohon ministan sadarwa, marigayi Arzika Tambuwal.

Source: Twitter
Ya kuma kasance cikin tawagar yaɗa labarai na manyan gungun siyasa kamar su People’s Front (PF) na marigayi Shehu Musa Yar’Adua, jam’iyyar SDP, DPP ƙarƙashin jagorancin Attahiru Bafarawa, da kuma gwamnatin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Haka zalika, ya bada gagarumar gudummawa a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ciki har da na Obasanjo/Atiku (1999 da 2003), Goodluck Jonathan/Namadi Sambo (2011), da Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa (2023).
Dingyadi, wanda ƙwararren ɗan jarida ne yana da gogewar fiye da shekaru 20, ya yi aiki da manyan kafafen yaɗa labarai kamar su Reporter/Nasiha, BBC Hausa, da wasu kafafe masu daraja a cikin gida da waje.
Wabara ya caccaki Damagum
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya soki Umar Iliya Damagum.
Wabara ya caccaki shugaban PDP na ƙasa ne kan dawo da Sanata Samuel Anyamwu a kan muƙamin sakataren jam'iyyar.
Ya nuna cewa dawo da Anyanwu kan muƙaminsa ya saɓa doka kuma wuce gona da iri ne a harkar shugabanci.
Asali: Legit.ng

