Akwa Ibom: PDP Ta Yi Babban Rashi Ranar Sallah, Gwamna Ya Sauya Sheka zuwa APC

Akwa Ibom: PDP Ta Yi Babban Rashi Ranar Sallah, Gwamna Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • A ƙarshe, Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya a yau Juma'a
  • Gwamna Eno ya sanar da haka ne a wani taro na musamnan da aka shirya a fadar gwamnatinsa da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom
  • Gwamnonin APC ƙarƙashin jagoranci Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne suka tarbi Fasto Umo Eno a hukumance

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da komawa APC mai mulki a hukumance.

Gwamna Eno ya sanar da sauya sheƙa ne a yau Juma'a, 6 ga watan Yuni, 2025 a fadar gwamnatinsa da ke Uyo, babban birnin Akwa Ibom a Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

Bayan jita jita na yawo, Wike ya magantu kan masu juya akalar gwamnatin Tinubu

Gwamna Umo Eno ya koma APC.
Bayan kamma shawarwari, Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Hoto: Pastor Umo Eno
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan gwamnan ya ce lokaci ya yi da zai bar PDP ya koma APC mai mulkin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Eno ya sauya sheka zuwa APC

An tattaro cewa Gwamna Eno ya shafe watanni yana tattaunawa da neman shawarwari daga jama'a da abokan siyasarsa kafin yanke hukuncin karshe.

A wani taron ganawa da jama’a da aka shirya a garin Ikot Abasi, Gwamna Eno ya ce:

“Lokaci ya yi da zan matsa zuwa mataki na gaba, na haɗe da APC. Lokaci ya yi da Akwa Ibom za ta daidaita da gwamnatin tarayya domin samar da damarmakin ci gaba ga al'umma.

Me yasa gwamnan Akwa Ibom ya koma APC?

Gwamnan ya bayyana cewa ya yanke hukuncin sauya sheƙa ne bayan watanni uku na shawara da tattaunawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki a fadin jihar.

Fasto Eno ya gode wa jam’iyyar PDP bisa goyon bayan da ta bashi a lokacin da yake mulki, amma ya ce lokaci ya yi da zai ɗauki sabon mataki na ci gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Osun ya gana da Tinubu kan shirin sauya sheƙa zuwa APC? An samu bayanai

Ya ƙara da cewa gamsuwa da salon mulkin Shugaba Bola Tinubu da bukatar ganin jihar Akwa Ibom ta yi daidai da gwamnatin tarayya su ne manyan dalilan da suka sa ya sauya sheƙa zuwa APC.

Gwamnan ya kuma tabbatar wa jama’ar jihar Akwa Ibom cewa zai ci gaba da aiki tukuru don amfaninsu, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.

“Bayan kammala zagayen neman shawara a matsayina na wanda kuka zaɓa ya maku hidima, na yanke shawarar sauya sheƙa zuwa APC domin ci gaban jihar,” in ji shi.
Gwamna Umo Eno ya bar PDP.
Gwamna Umo Eno ya ce salon mulkin Bola Tinubu ne ya ja ra'ayinsa zuwa APC Hoto: Pastor Umo Eno
Source: Facebook

Gwamnonin APC sun halarci taron sauya sheƙar

Gwamnonin APC karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyya mai mulki kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma ne suka karɓi Fasto Umo Eno a hukumance.

The Cable ta tattaro cewa gwamnonin da suka je Uyo don shaida sauya sheƙar Gwanna Eno sun haɗa da Bassey Otu na Jihar Kuros Riba Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos da kuma Dapo Abiodun na Jihar Ogun.

Sauran da suka halarta sun hada da Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, Monday Okpebholo na Jihar Edo, da Francis Nwifuru na Jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaɓe, Gwamna ya yi martani kan zargin ziyartar boka domin neman zarcewa

Gwamna Eno zai kaucewa binciken EFCC

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa zai yi taka tsan-tsan domin kaucewa binciken hukumar EFCC bayan ya bar mulki.

Gwamna Eno ya ce ba zai aikata abin da zai EFCC ta gayyace shi ba, yana mai cewa zai tafiyar da dukiyar al'umma cikin gaskiya da rikon amana.

Umo Eno ya danganta matsalar da yawancin tsofaffin gwamnoni ke shiga bayan mulki da matsin lambar da jama'a ke yi musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262