An 'Bankado' Yadda APC ke Firgita 'Yan Adawa, Tana Jawo Su cikinta Karfi da Yaji
- Shugabar kwamitin rikon kwarya ta LP, Sanata Nenadi Usman ta yi zargin cewa APC na amfani da miyagun dabaru a kan yan adawa
- A cewarta, jam'iyya mai mulki na matsawa manyan yan adawa su koma cikinta bayan ta yi masu barazana da amfani da hukumomin gwamnati
- Ta bayyana cewa wannan dabi'a a raunata adawa, duk da cewa su ma 'yan adawa na taka rawa wajen kara gurgunta tafiyarsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugabar kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar LP, Sanata Nenadi Usman, ta zargi APC da amfani da dabaru iri-iri don hana ci gaban jam’iyyun adawa da kuma rage karfinsu a siyasar Najeriya.
A cewar ta, APC na amfani da barazana, danniya, da cin zarafi ta wasu hanyoyi daban-daban don kakabawa 'yan adawa takunkumi, lamarin da ke raunana dimokuraɗiyya a ƙasar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Nenadi Usmanta yi wannan furuci ne yayin liyafar cin abinci da raba kyaututtuka na ADC da aka gudanar a Abuja a ƙarshen mako.
‘Jam'iyyar APC na tauye adawa,’ Nenadi Usman
Sahara Reporters ta wallafa Sanata Nenadi Usman ta kara da cewa APC na amfani da hukumomin gwamnati da kuma dukiyar ƙasa wajen tilasta 'yan adawa su bi doka da tsarin da jam’iyyar ke so.
Tsohuwar Ministar Kudin ta ce irin waɗannan dabaru na hana adawa tsayawa da ƙafarta, musamman ganin yadda aka fara matsa wa 'yan adawa lamba don su koma APC.
Ta ce:
“Tun bayan da APC ta karɓi mulki a matsayin jam’iyya mai ci, aka fara kitsa wata gagarumar manufa don rage karfin adawa a ƙasar nan.”
Nenadi: "APC ta raunata dimokuradiyya"
Nenadi Usman ta ce tsarin siyasar da ke amfani da albarkatun gwamnati don haddasa rigima a cikin jam’iyyun adawa na nuna cewa ana son mamaye komai da karfi da yaji.

Source: Facebook
Ta ce:
“Ba za mu iya kiran kanmu masu dimokuraɗiyya ba muddin ba mu da adawa mai ƙarfi da ke aiki yadda ya kamata. A duniya, adawa ce ke ɗaga tutar sauyi da dorewar siyasa, amma a nan Najeriya, ana kokarin dakile muryoyin adawa a hankali kuma da gangan."
Ta bukaci jam’iyyun adawa a Najeriya da su manta da son rai, girman kai da rabuwar kawuna, su mayar da hankali kan samar da ingantaccen zaɓi ga al’umma.
Sanata Nenadi ta ƙara da cewa:
“Sau da yawa, adawa ce ke haddasa raunin kanta."
APC ta magantu kan takarar majalisa
A wani labarin, mun wallafa cewa APC ta nesanta kanta daga rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ta ba dukkanin 'yan majalisar tarayya damar sake tsayawa takara.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Felix Morka, ya fitar a ranar Talata, ya bayyana rahoton a matsayin labarin bogi da aka kirkira don jawo rudani.
Jam’iyyar ta kuma bukaci 'ya'yanta da al’ummar kasa gaba ɗaya da su yi watsi da rahoton, tana mai cewa an kirkire shi ne domin a hada husuma da jawo rudani a cikin jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

