"Zama Daram": Sanata Ya Sha Alwashin Kin Ficewa daga PDP, Ya Ambaci Dalili

"Zama Daram": Sanata Ya Sha Alwashin Kin Ficewa daga PDP, Ya Ambaci Dalili

  • Sanatan PDP mai wakiltar Cross Rivers ta Arewa a majalisar dattawa, Jarigbe Agom Jarigbe, ya ce zai ci gaba da zama a jam'iyyar
  • Jarigbe Agom Jarigbe ya bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa a PDP domin hakan shi ne abin da mutanen mazaɓarsa suke so
  • Hakazalika ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya amince da batun ƙirƙiro jihar Ogoja domin a cewarsa hakan zai zama abin tarihi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Cross Rivers - Jarigbe Agom Jarigbe, mai wakiltar Cross Rivers ta Arewa a majalisar dattawa, ya sake jaddada mubaya’arsa ga jam’iyyar PDP.

Sanata Jarigbe Agom Jarigbe ya sha alwashin cewa ba zai sauya sheƙa ba duk da yawan ficewar da ake yi daga jam’iyyar PDP a halin yanzu.

Jarigbe Agom Jarigbe
Sanata Jarigbe ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP ba Hoto: Sen Jarigbe Agom For All
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da mambobin ƙungiyar ƴan jarida ta jihar Cross Rivers (CROSSJOF) a ziyarar girmamawa da suka kai masa a gidansa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Akwai babbar barazana ga APC,' Babban lauya ya fadi abin da zai kifar da Tinubu

Meyasa Sanata Jarigbe ba zai bar PDP ba?

Sanata Jarigbe ya bayyana cewa biyayyarsa tana ga mutanensa na mazaɓar da yake wakilta, waɗanda har yanzu ke ci gaba da zama daram a PDP, rahoton jaridar Thisday ya tabbatar.

“Siyasarmu ta dogara ne da matsayar al’umma. Idan na koma gida na ce musu zan sauya sha, za su ce, ‘To ka tafi, amma ba za mu bi ka ba.’"
"Mutanena na son su ci gaba da kasancewa a cikin PDP, ni kuma zan tsaya tare da su. Ba wai saboda faɗa da wani ba ne, sai dai don girmama muradin mutanen mazaɓata."

- Sanata Jarigbe Agom Jarigbe

Duk da cewa bai ga laifin waɗanda suka sauya sheƙa daga jam’iyyunsu ba, ya ce yana yiwuwa hakan yana da nasaba da buƙatun al’ummarsu.

Sanatan na jam’iyyar adawa ya buƙaci mutanen mazaɓarsa da su goyi bayan gwamnatin jihar da jam’iyyar APC ke jagoranta, domin ganin cewa sun samu romon dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Na hannun daman Obi ya fice daga LP, zai taya APC nemawa Tinubu kuri'u a 2027

“Dole ne mu guji rikice-rikice, mu marawa gwamnatin jiha baya domin mulki ya isa ga kowa da kowa."

- Sanata Jarigbe Agom Jarigbe

Sanata Jarigbe Agom Jarigbe
Sanata Jarigbe ya ce zai ci gaba a PDP don mutanensa Hoto: Sen Jarigbe Agom For All
Source: Facebook

Sanatan PDP ya miƙa buƙatarsa ga Tinubu

Sanatan ya kuma yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya duba buƙatar ƙirƙiro jihar Ogoja, yana mai cewa yankin shi ne kaɗai tsohon lardi a Najeriya da ba ya da jiharsa.

“Idan akwai wata jiha da ya kamata a kirkira a Najeriya, to Ogoja ce. Ina da yaƙinin cewa shugaban ƙasa zai saurare mu. Kirkiro jiha a lokacin mulkin dimokuradiyya zai kasance abin tarihi."

- Sanata Jarigbe Agom Jarigbe

Gwamna Eno ya shirya barin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya sake nuna alamun ficewa daga jam'iyyar PDP.

Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa yana son jam'iyyar PDP har cikin zuciyarsa, amma lokaci ya yi da zai fice daga cikinta.

Sai dai, gwamnan bai ambaci jam'iyyar da zai koma idan ya tattara ya fice PDP wacce ya lashe zaɓen gwamna ƙarƙashinta a shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng