2027: Wasu 'Yan Majalisa Sun Yi Watsi da Hadaka, Sun Goyi Bayan Tazarcen Tinubu
- ’Yan majalisar tarayya daga jihar Cross River sun amince da tazarcen Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Bassey Otu a 2027
- Sun bayyana cewa Tinubu ya cancanci karin wa’adin shugabanci bisa ayyukan raya kasa da ya aiwatar, musamman gina hanyar tekun Lagos-Calabar
- Haka zalika sun ce gwamna Otu ma ya samu gagarumar nasara a fannin tsaro da ilimi a jihar, don haka ya cancanci ci gaba da mulki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - ’Yan majalisar tarayya daga Cross River sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Bassey Otu domin su sake tsayawa takara a zaben 2027.
’Yan jam’iyyar APC daga jihar Cross River ne suka sanar da haka yayin wata ganawa da manema labarai a Calabar.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa 'yan majalisar sun ce matakin na nuna yarda da gamsuwa da irin mulkin da shugabannin ke yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban 'yan majalisar kuma Sanata mai wakiltar Cross River ta Tsakiya, Eteng Williams, ya ce sun dauki matakin ne don hadin kai da cikakken nazari kan yadda abubuwa ke tafiya.
'Yan majalisa sun yaba da ayyukan Tinubu
Eteng Williams ya ce a matsayinsu na wakilan jama’a, sun gamsu da ayyukan da Tinubu ke gudanarwa, musamman aikin hanyar tekun Lagos-Calabar da kudirin lamunin karatu ga ɗalibai.
Sanata Eteng Williams:
“Mun yarda cewa shugaban kasa ya yi kokari, musamman wannan babbar hanyar da za mu amfana da ita.
"Don haka muna mara masa baya don ya kammala wannan aiki a wa’adi na biyu.”
Sanatan ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya nuna kwazo da jarumtaka a fannonin tattalin arziki, man fetur, da kuma ci gaban yankuna daban-daban na kasar nan.
Gwamna Otu ya samu yabo kan tsaro da ilimi
Game da Gwamna Bassey Otu kuwa, Sanata Williams ya ce an samu ci gaba a jihar Cross River karkashin jagorancinsa.
Sanatan ya ce gwamnan ya sabunta ɗakin karatu na jihar da kuma kaddamar da Operation Okwok don inganta tsaro.
Eteng Williams ya ce:
“A yau abin da muka gani ya isa mu ce an samu cigaba, mu nemi Otu ya ci gaba da aiki. Ya cancanci karin wa’adi bisa yadda ya tunkari manyan matsaloli a jihar.”

Source: Twitter
Dalilin goyon bayan Tinubu a Cross River
Hon. Mike Etaba, mai wakiltar Obubra/Etung, ya ce goyon bayan zai ba shugabannin damar mayar da hankali kan gudanar da mulki ba tare da cikas ba.
Bassey Akiba, dan majalisar Calabar Municipality/Odukpani, ya ce matakin ya dace da dabi’ar dimokuradiyya kuma yana nuna hadin kai da fahimta a tsakanin bangaren dokoki da zartaswa.
Gwamna Fubara ya yaba wa Bola Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Siminalayi Fubara da aka dakatar a River ya yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Fubara ya ce kokarin da Tinubu ya yi a Rivers wajen saka dokar ta baci ya jawo hana samun rikici a jihar.
Fubara ya kara da cewa yana da tabbas a kan cewa zai dawo gwamna a nan kusa kadan kuma za a yi sulhu tsakaninsa da Nyesom Wike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


