Na Hannun Daman Obi Ya Fice daga LP, Zai Taya APC Nemawa Tinubu Kuri'u a 2027

Na Hannun Daman Obi Ya Fice daga LP, Zai Taya APC Nemawa Tinubu Kuri'u a 2027

  • Fabian Ozoigbo ya fice daga LP ya koma APC a Anambra, yana yabawa Tinubu kan yadda ya daidaita tattalin arziki bayan cire tallafi
  • Ozoigbo ya ce LP na da matsalar rashin gaskiya, yana ganin tattalin arzikin Najeriya bai rushe ba kamar yadda aka zata a baya
  • Yana ganin Ukachukwu da Ekwunife za su taimaka wa APC lashe zaben Anambra, yana mai cewa ya na son shiga sabuwar tafiyar ci gaba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Fabian Ozoigbo, ɗaya daga cikin na hannun daman ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, ya fice daga jam’iyyar, ya koma APC a Anambra.

Ozoigbo, wanda ya shugabanci ɓangaren dabarun sufuri a LP, ya ce ya dawo goyon bayan Shugaba Bola Tinubu saboda yadda ya ke ƙoƙarin tafiyar da ƙasar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027

Wani na hannun daman Peter Obi ya fice daga LP zuwa APC, zai yiwa Tinubu aiki a 2027
Tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi tare da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Na hannun daman Peter Obi ya koma APC

Ya zargi LP da rashin gaskiya, yana mai cewa jam’iyyar ta nuna rashin amincewa da sakamakon zabe da INEC ta bayyana, wanda bai dace ba, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana da manema labarai a Awka ranar Laraba, Ozoigbo ya ce a matsayinsa na ɗan adawa, ya zata tattalin arzikin Najeriya zai rushe bayan cire tallafin fetur.

Sai dai ya ce ya yi mamaki yadda shugaban ƙasa Tinubu ya samu damar daidaita tattalin arzikin, duk da ƙalubale da wahalhalun da ake ciki.

Ozoigbo ya ce:

“A matsayin ɗan adawa, na zata tattalin arzikin zai rushe gaba ɗaya bayan cire tallafin fetur, amma abin mamaki tattalin arzikin yana kan mizani mai kyau.”

Dalilin Ozoigbo na son zama a cikin APC

Daily Post ta rahoto Ozoigbo yana cewa:

“Na yanke shawarar komawa cikin gwamnatin da ke kokarin daidaita tattalin arzikin don ba da tawa gudunmawar, kuma kasancewata a cikin gwamnatin, zai wanke zarge-zarge na.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan APC ya fadi dalilin da ya sa Tinubu ke samun goyon baya

“Buri na shi ne na zama cikin sabon tsari na farfado da Najeriya, kamar yadda mai girma Tinubu ya ke bullo da manufofin da za su farfaɗo da tattalin arziki.
"Tun da tattalin arzikin bai rushe ba kuma alamu na farfaɗowa suna bayyana, ina so na zama cikin wannan abin mamaki na gwamnati mai ci."

Ya ce komawarsa APC ta zo a daidai lokacin da Anambra ke shirye-shiryen zaben gwamna da za a yi ranar 8 ga Nuwamba, inda ya ce jam'iyyar za ta yi nasara idan Prince Nicholas Ukachukwu, ne ɗan takarar ta.

Fabian Ozoigbo ya ec yana son yi wa APC aiki a 2027 domin ya gamsu da ayyukan gwamnatin Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Ozoigbo ya gamsu da dan takarar APC a Anambra

Ozoigbo ya ce ba Ukachukwu tikitin takara tare da shigowar Sanata Uche Ekwunife cikin jam'iyyar za su sauƙaƙa wa APC samun nasara a zaben gwamnan mai zuwa.

“A baya-bayan nan, APC ta fito da gwarzon ɗan takara, Prince Nicholas Ukachukwu, wanda ya shahara a cikin jama’a.
“Fitowarsa, tare da ayyukan jin ƙai da ya dade yana yi, sun fara jawo hankalin mutane, musamman ‘yan ƙasa masu matsakaicin hali. Ni da mutanena muna son mu kasance cikin wannan tafiya.”

Kara karanta wannan

Malami: Ministan Buhari yi yi wa Tinubu, Ganduje da 'yan APC rubdugu kan tsaro

- Fabian Ozoigbo.

Jam'iyyar LP ta yi watsi da hadakarsu Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar LP ta bayyana cewa ba ta da hannu a kowane shirin haɗaka da jam’iyyun siyasa, ciki har haɗakarsu Atiku Abubakar.

Ta bukaci Peter Obi da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar su kauce wa irin waɗannan haɗin gwiwa da ba su da amincewar uwar jam’iyya.

Jam’iyyar ta bayyana halartar Obi wajen taron haɗin gwiwa ba tare da sahalewa ba a matsayin raini ga shugabanci da karya tsarin dokokin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com