Bola Tinubu Ya Sha Yabo da Ya Sace Gwiwar Nyesom Wike a Abuja

Bola Tinubu Ya Sha Yabo da Ya Sace Gwiwar Nyesom Wike a Abuja

  • Dele Momodu ya jinjinawa Shugaba Bola Tinubu kan matakin dakile rufe ofishin jam’iyyar PDP da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi yunkurin aiwatarwa
  • Momodu ya ce matakin ya nuna cewa Wike ba shi da cikakken iko, kuma Tinubu ne kadai shugaban kasa da ke da hurumin yanke irin wannan hukunci
  • Gogaggen dan siyasar ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya hana Nyesom Wike cigaba da kawo rudani a mulkin gwamna Siminalayi Fubara a jihar Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban ɗan jarida, Dele Momodu ya nuna matuƙar jin daɗinsa da yadda Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Ministan Abuja, Nyesom Wike, daga rufe sakatariyar PDP.

A jiya Litinin hukumar FCTA karkashin Nyesom Wike ta jagoranci rufe sakatariyar PDP da wasu kadarori a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

A karon farko, Shugaba Tinubu ya taka wa Wike birki a harkokin gudanarwa a Abuja

Dele Momodu
Momodu ya yabawa Tinubu kan dakatar da Wike rufe ofishin PDP. Hoto: Dele Momodu| Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Dele Momodu ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya fadi haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar a Amurka, inda ya ce hakan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Wike ba shugaban kasa ba ne, kuma ba shi da ikon cin karen sa babu babbaka.

Wike ya zamewa Tinubu kaya inji Momodu

Momodu ya bayyana cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya zama kaya mai nauyi ga gwamnatin Tinubu saboda yawan shiga rikice-rikicen siyasa da nuna girman kai.

Ya ce ko da yake babu wanda ya kamata ya ƙi biyan haraji ko hakkokin gwamnati, amma ya kamata a rika bin abubuwa a sannu sannu.

Momodu ya ce ba daidai ba ne a rika amfani da karfin iko wajen nuna ƙiyayya da ɗaukar matakai da ke da alamar ramuwar gayya, musamman akan manyan jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi magana yayin da aka hana shi shiga Saudiyya aikin Hajji

Ya kara da cewa akwai sauran manyan ministoci kamar Dave Umahi da ke aiki sosai, amma suna gudanar da aikinsu cikin ladabi da kwanciyar hankali ba tare da tada kura ba kamar Wike.

An bukaci Tinubu ya sake duba rikicin Ribas

A cikin sanarwar tasa, Momodu ya koka kan yadda Wike ke ci gaba da tsoma baki a harkokin gwamnatin jihar Ribas.

Dele Momodu ya ce da Shugaba Tinubu ya dakile hakan tun farko, da an kare al’ummar jihar daga fuskantar rudani da ake ciki yanzu.

Ya roki Shugaba Tinubu da ya cigaba da nuna iko da jagoranci wajen hana kowane jami’in gwamnati yin abin da ya fi karfinsa ko kuma ya janyo rikici a cikin kasa.

Dele Momodu
An bukaci Tinubu ya sake duba rikicin Ribas. Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

Wike ya warware yarjejeniyar da PDP ta yi

A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce ya fita daga duk wani sharadi da aka yi da shi a PDP.

Ministan ya ce ya taimaki da yawa daga cikin gwamnonin PDP amma a yanzu suna so su juya masa baya saboda siyasa.

Nyesom Wike ya ce zai cigaba da fafutukar kawo dalaci a PDP kasancewar an ci amarsa musamman bayan kafa kwamitin sulhu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng