"Za Su Sha Mamaki": An Hango Abin da Zai Faru da APC a Zaben 2027

"Za Su Sha Mamaki": An Hango Abin da Zai Faru da APC a Zaben 2027

  • Ana ci gaba da muhawara kan yadda zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ake tunkara zai kaya a ƙasar nan
  • Jigo a jam'iyyar PDP kuma jagoran tafiyar 'The Alternative', Segun Sowunmi, ya hango makomar APC a zaɓen shugaban ƙasa
  • Segun Sowunmi ya bayyana cewa APC za ta sha mamaki a zaɓen duba da yadda take cika baki a fagen siyasar ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jagoran ƙungiyar 'National Opposition Movement Coalition' (NOMC) wadda ake yi wa laƙabi da “The Alternative,” Segun Sowunmi, ya gargaɗi jam'iyyar APC.

Segun Sowunmi ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta sha mamaki a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 idan har ta ci gaba da cika bakin samun nasara ba tare da yin bincike ba.

Segun Sowunmi
Segun Sowunmi ya ce APC za ta sha mamaki a 2027 Hoto: Segun Sowunmi
Source: Facebook

Segun Sowunmi ya bayyana hakan ne a jihar Katsina bayan ya ziyarci yankin Arewacin Najeriya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

2027: Ana shirin hadaka, Peter Obi ya fara magana kan hakura da takura

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sowunmi ya ce APC za ta ga abin mamaki a 2027

Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana shakku dangane da yadda jama’a ke karɓar shugaban ƙasa Bola Tinubu.

“Ina duba yadda ake karɓar Shugaba Bola Tinubu a wannan yanki, waɗanda ke alfahari ba tare da yin bincike ba za su yi mamaki. Ba za ka ci zabe ba da tunanin za a haɗa maka ƙuri’u ba kawai."

- Segun Sowunmi

Ya nuna damuwarsa game da yadda APC ke yin magana cikin alfahari da girman kai.

Sowunmi ya buƙaci a samar da tsayayyen ɗan takara

Segun Sowunmi ya roƙi masu ruwa da tsaki da su fitar da ɗan takarar da za a amince da shi ba tare da nuna son rai ko wariya ba, yana mai cewa:

"Wannan ne dalilin da yasa muka ƙirƙiro da tafiyar ‘The Alternative’. Za mu yi amfani da wannan dandali wajen tallata ɗan takarar da mutane suke so."

Kara karanta wannan

Daga fara maganar hakaɗa a ADC, ana zargin gwamnan APC ya fara shirin komawa

Ya jaddada cewa gina magoya baya na gaskiya yana buƙatar lokaci da ƙoƙari, tare da godewa jama’a masu yawa da suka halarci taron kuma suka rungumi tafiyar.

Segun Sowunmi
Segun Sowunmi ya bukaci a yi addu'a kan rashin tsaro Hoto: Segun Sowunmi
Source: Facebook

Jagoran na NOMC ya kuma bayyana damuwa kan matsalar rashin tsaro a ƙasar nan, inda ya buƙaci mahalarta taron da su yi addu’a domin Allah Ya kawo ƙarshen munanan ayyukan masu aikata sharri.

Jawaban Segun Sowunmi sun biyo bayan ƙaddamar da tafiyar “The Alternative” da aka yi a Abuja a watan Nuwamba 2024, da nufin ceto dimokuradiyyar Najeriya.

Tsohon sanata ya yi watsi da haɗaka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanata mai wakiltar Osun ta Yamma a majalisar dattawa, Mudashiru Husain, ya yi fatali da haɗakar jam'iyyun adawa.

Sanata Mudashiru Husain ya bayyana cewa jagororin haɗakar ba su da haɗin kai da kishin ƙasan da ake buƙata don jagorantar irin wannan tafiya.

Hakazalika ya bayyana cewa babu wata haɗaka komai girmanta da za ta iya raba Shugaba Bola Tinubu da mulkin Najeriya a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng