Rivers: Komai na Iya Faruwa da Rigima Ta Kunno Kai a Kokarin Dawo da Fubara

Rivers: Komai na Iya Faruwa da Rigima Ta Kunno Kai a Kokarin Dawo da Fubara

  • Rikici ya sake kunno kai a jihar Rivers yayin da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike ke neman rushewa
  • Wata rigima ta barke lokacin wani taron mata wanda uwargidan Shugaban Kasa ta shirya, inda mata suka fice daga wurin suna nuna rashin jin daɗi
  • Yayin da Wike ya soki lamarin, kungiyoyin mata da na Ijaw sun kare kansu, suna cewa ba Fubara ne ya shirya musu hakan ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Sabuwar rigimar siyasa ta kunno kai a Jihar Rivers da ke jefa shakku kan yiwuwar dawowar Gwamna Siminalayi Fubara.

A baya, an dakatar da Fubara ne bayan Bola Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci na tsawon wata shida.

Taba kimar Remi Tinubu ka iya hana dawo da Fubara
Bayan yi wa Remi Tinubu rashin kunya, ana zargin hakan zai kawo matsala a ƙoƙarin dawo da Fubara. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Rigimar da ke neman jawowa Fubara matsala

Wasu masu ruwa da tsaki sun yi tsammanin Shugaba Tinubu zai sanar da dawowar Fubara a jawabinsa na ranar dimokradiyya 29 ga watan Mayu, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

An faɗi ranar da ake son dawo da Fubara bayan taso Tinubu a gaba, ya nemi afuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai abubuwan da ke faruwa yanzu sun jawo matsala kan wannan fata da ake yi na mayar da Fubara mulkinsa.

Farkon rigimar ta faru a ranar Juma’a yayin wani shiri na karfafa mata 500 na Jihar Rivers da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta shirya.

Matan da aka zaɓa don amfana sun fita daga wurin taron da aka Port Harcourt, suna nuna rashin jin daɗi ga wakilcin uwargidanshugaban rikon kwarya.

Dr. Theresa Ibas ce ta wakilci uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu a wurin inda aka samu hatsaniya da ya jawo hankalin ƙasa baki ɗaya.

Ana tunanin za a samu matsala a ƙoƙarin dake da Fubara mulki
Taba kimar Remi Tinubu na neman jawo matsala da ake rokon dawo da Fubara mulki. Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Wike ya soki Fubara a Rivers

Ministan Babban Birnin Tarayya, Barista Nyesom Wike, wanda ke ziyarar aiki a China, ya soki lamarin, yana cewa hakan cin mutunci ne ga Shugaban Ƙasa.

Ya ce:

“Cin mutunci ga wakiliyar Uwargidan Shugaban Ƙasa da Ofishin Shugaban Ƙasa da Kwamandan Rundunar Soji, ina mai ba da hakuri a madadin jihar Rivers."

Kara karanta wannan

Wike ya zargi gwamna Fubara da jawo wulakanta matar Tinubu a Rivers

Kakakin 'Ijaw Republican Assembly', Annkio Briggs ta ce an yi ƙoƙarin ɗora laifi ga Gwamna Fubara ba bisa ƙa’ida ba.

Ta ce:

“Zargin Gwamna Fubara kamar kirkiro wa kare suna mara kyau ne domin a kashe shi."

Briggs ta ƙara da cewa matan da ke karkashin kungiyar 'Rivers Women Unite for Sim' sun shirya tarbar uwargida Tinubu da cikakken goyon baya.

A martaninsu, matan sun fitar da sanarwa cewa:

“Gwamna Fubara bai da hannu a abinda muka aikata. Mu ‘yan asali ne, ba kuraye ba.”

Wannan sabon rikicin, ya nuna cewa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Fubara da Wike ta karye, kuma hakan na iya hana Fubara komawa ofis a kusa.

An bukaci Tinubu ya dawo da Fubara

A baya, kun ji cewa wasu rahotanni sun ce an taso shugaban kasa, Bola Tinubu a gaba bayan sanya dokar ta-ɓaci a Rivers.

Gwamna Siminalayi Fubara ya sauko daga matsayinsa ya nemi gafara daga Nyesom Wike a gidansa dake Abuja don sasanta rikicin siyasar jihar.

Bayan ganawa da shugaba Tinubu, Fubara ya nuna nadama tare da neman zaman lafiya ba tare da goyon bayan dattawan Rivers ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.