Zaben 2027: Gwamnonin PDP Sun Bayyana Matsayarsu kan Hadaka don Kayar da Tinubu

Zaben 2027: Gwamnonin PDP Sun Bayyana Matsayarsu kan Hadaka don Kayar da Tinubu

  • Gwamnonin PDP sun gudanar da taro domin tattauna batutuwan da suka shafi makomar jam'iyyar a birnin Ibadan na jihar Oyo
  • Ƙungiyar gwamnonin ta bayyana cewa ba za ta shiga wata haɗaka da ake shirin samarwa ba ta jam'iyyun adawa
  • Gwamnonin na PDP sun kuma sake nuna goyon bayansu ga gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara wanda aka dakatar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun yi magana kan shirin haɗakar da jam'iyyun adawa ke yi don ƙwace mulki a hannun APC da Shugaba Bola Tinubu.

Gwamnonin na PDP sun bayyana ƙin amincewarsu da shirin haɗa ƙawance da wasu jam’iyyu domin ƙalubalantar jam’iyyar APC kafin babban zaɓen 2027.

Gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP sun yi watsi da batun hadaka Hoto: @seyimakinde
Asali: Twitter

Gwamnonin PDP sun yi taro a Ibadan

Shugaban taron kuma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ne ya karanta sanarwar wacce aka sanya a shafin X na PDP ga manema labarai.

Kara karanta wannan

El Rufa'i: Dukkan shugabannin APC a mazabar Kaduna sun koma SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan matsayar na daga cikin abubuwan da suka cimmawa a taron gwamnonin PDP da aka gudanar a birnin Ibadan, jihar Oyo daga ranar Lahadi zuwa Litinin.

Ƴan takarar shugaban kasa na PDP da LP a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar da Peter Obi, suna ƙoƙarin kafa haɗaka domin ƙwace mulki daga hannun APC a shekarar 2027.

Gwamna Mohammed ya bayyana cewa sun buɗe kofar maraba ga kowa ko jam’iyyar da ke da sha’awar shiga PDP.

Menene matsayar gwamnonin PDP kan haɗaka?

"Mun lura da yaɗuwar jita-jita a faɗin ƙasa dangane da yiwuwar haɗewar jam’iyyu, ƙungiyoyi ko gamayyar wasu, inda muka cimma matsayar cewa ba za mu shiga kowane ƙawance ko haɗaka ba."
"PDP a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa, tana maraba da kowace jam’iyya, mutum, ko ƙungiya da ke da niyyar shiga jam’iyyar domin fafutukar ƙwato mulki da samar da nagartaccen shugabanci a shekarar 2027."

- Gwamna Bala Mohammed

Kara karanta wannan

APC ta tabo batun ajiye Kashim Shettima, ta ba Shugaba Tinubu shawara

Gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP sun nuna goyon baya ga Gwamna Fubara Hoto: @seyimakinde
Asali: Twitter

Gwamnonin sun kuma sake jaddada matsayinsu dangane da muƙamin sakataren jam’iyyar na kasa, inda suka ƙi amincewa da Sam Okoye ko Samuel Anyanwu su ci gaba da riƙe kujerar.

Sun bada shawarar cewa mataimakin sakatare na ƙasa na PDP ya ci gaba da aiki a matsayin muƙaddashin sakatare har zuwa lokacin da za a gabatar da sabon sakatare daga yankin Kudu Maso Gabas don tantancewa da amincewa a taro na gaba.

Gwamna Fubara ya samu goyon baya a PDP

Sanarwar ta kuma bayyana goyon bayansu ga gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, Siminalayi Fubara, inda ta bayyana cewa:

"Muna sake bayyana aniyarmu ta goyon bayansa har zuwa ƙarshe yayin da yake fuskantar matsalolin da suka taso sakamakon ayyana dokar ta ɓaci a jiharsa."

PDP ta ƙi amincewa da murabus ɗin kakakinta

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo ta ƙi amincewa da murabus ɗin mai magana da yawun bakinta.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi fallasa, ya tono shirin Sanata Ndume kan jam'iyyar APC

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa ba za ta amince da murabus ɗin da Kennedy Peretei ya yi ba daga muƙaminsa.

Shugabannin PDP a jihar sun buƙaci Kennedy Peretei da ya haƙura da batun yin murabus domin yana da matuƙar muhimmanci a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng