Jiga Jigan APC Sun Fadi Gwamnan PDP da ba Su Maraba da Shi a Jam'iyya

Jiga Jigan APC Sun Fadi Gwamnan PDP da ba Su Maraba da Shi a Jam'iyya

  • Jam'iyyar APC a jihar Delta ta samu ƙaruwa bayan mambobin wata ƙungiyar siyasa sun sauya sheƙa zuwa cikinta
  • A yayin tarbarsu, Ned Nwoko ya bayyana cewa ba su maraba da Gwamna Sheriff Oborevwori zuwa cikin jam'iyyar APC
  • Sanatan ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta shirya raba gwamnan da jam'iyyarsa ta PDP daga mulkin jihar Delta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa ba su maraba da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, zuwa cikin jam'iyyar APC.

Sanata Ned Nwoko ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta kayar da gwamnan da jam’iyyarsa ta PDP a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

Ned Nwoko, Sheriff Oborevwori
Sanata Ned Nwoko ya ce ba su yin maraba da Gwamna Oborevwori zuwa APC Hoto: Ned Nwoko, Rt. Hon Sheriff Oborevwori
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Ned Nwoko ya bayyana hakan ne yayin wani taron siyasa a Agbor da ke jihar Delta.

Kara karanta wannan

APC ta tabo batun ajiye Kashim Shettima, ta ba Shugaba Tinubu shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta samu ƙaruwa a Delta

Taron ya ƙunshi sauya sheƙar mambobin ƙungiyar Delta Unity Group (DUG) daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Taron, wanda ake ganin yana da muhimmanci wajen sake fasalin siyasar jihar Delta, ya samu halartar manyan shugabannin APC.

Daga cikin mahalarta taron akwai shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege.

Ba a maraba da Gwamna Oborevwori a APC

Yayin da yake magana a wajen taron, Sanata Nwoko ya bayyana cewa Gwamna Sheriff Oborevwori yana son shigowa cikin jam'iyyar APC.

“Oborevwori yana so ya shigo APC, amma ku gaya masa ya zauna inda yake. Za a kayar da shi. Ba ma son shi a cikin APC.”

- Sanata Ned Nwoko

Duk da cewa tawagar yaɗa labarai ta Gwamna Oborevwori na ci gaba da musanta jita-jitar sauya sheƙarsa zuwa APC, Nwoko da Omo-Agege sun nace cewa APC ba za ta karbi gwamnan ba ko tsohon Gwamna Ifeanyi Okowa.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi fallasa, ya tono shirin Sanata Ndume kan jam'iyyar APC

Omo-Agege ya ce fiye da kashi 60% na mambobin PDP sun riga sun koma APC a jihar Delta tun daga shekarar 2023, lamarin da ke ƙara karfin jam’iyyar a fagen zaɓen 2027.

Gwamna Oborevwori
'Yan APC ba su maraba da gwamnan Delta zuwa cikin jam'iyyar Hoto: @SheriffOborevwori
Asali: Twitter

APC ta shirya ƙwace mulkin Delta daga hannun PDP

Sanata Nwoko ya ƙara da cewa dole ne mulkin PDP na tsawon shekaru 25 a jihar Delta ya zo larshe, yana mai cewa dole sai gwamnan na gaba ya fito daga APC.

Haka kuma ya jaddada goyon bayansa ga kirkiro sabuwar jihar Anioma, inda ya zargi PDP da hana ruwa gudu kan ƙudirin.

Masana na ganin karɓar Oborevwori cikin APC na iya fusata masu kaɗa ƙuri’a da ke buƙatar sauyi, inda suka yi gargaɗin cewa hakan na iya raunana damar APC a 2027.

Sauya sheƙar mambobin ƙungiyar DUG ya ƙara ƙarfafa tasirin APC a jihar Delta.

APC ta ba Tinubu shawara kan Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Borno ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ka da ya ajiye Ƙashim Shettima.

Kara karanta wannan

Babban kusa a APC ya ba 'yan adawa sirrin kayar da Tinubu a 2027

Jam'iyyar APC ta buƙaci shugaban ƙasan da ya ci gaba da tafiya da Shettima domin su yi takara tare a zaɓen shekarar 2027.

Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sun nuna irin sadaukarwa da gudunmawar da Shettima ya ba da wajen kafa gwamnatin Bola Tinubu a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng