'Fubara zai Dawo Kujerarsa nan kusa,' Abokin Wike Ya Yi wa 'Yan Rivers Albishir

'Fubara zai Dawo Kujerarsa nan kusa,' Abokin Wike Ya Yi wa 'Yan Rivers Albishir

  • Tsohon shugaban kungiyar MEND ya ce Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers zai dawo kan kujerarsa, duk da rikicin siyasar da ke ci gaba a jihar
  • Thomas Ekpemupolo da aka fi sani da Tompolo ya fadi haka ne a bikin cikarsa shekaru 54, inda ya ce yana kan kokarin sasanta Fubara da Nyesom Wike
  • Ya kuma karyata zargin da ake yi masa na cin amanar al’ummar Ijaw, yana mai cewa rayuwarsa gaba ɗaya sadaukarwa ce domin kare mutuncin kabilar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A karon farko tun bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, babban jagoran Ijaw kuma tsohon shugaban kungiyar MEND, Thomas Ekpemupolo (Tompolo) ya yi magana.

Tompolo ya yi magana kan rikicin Rivers inda ya tabbatar da cewa Gwamna Siminalayi Fubara zai dawo bakin aiki gaba kadan.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi ainihin abin da ya kai Bola Tinubu Faransa

Fubara
Tompolo ya yi albishir da cewa Fubara zai dawo bakin aiki. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Tompolo ya bayyana haka ne a ranar Asabar, yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan magana kan siyasar Rivers, Tompolo ya kuma yi jawabi game da halin siyasar yankin Neja Delta da rahoton raba mazabun Delta da aka ce INEC za ta yi.

Ya ce ya yi shiru ne domin ba ya son hura wutar rikici, amma yanzu lokaci ya yi da zai bayyana matsayarsa tare da tabbacin cewa ba zai taba cin amanar al’ummar Ijaw ba.

Tompolo ya yi karin haske kan rikicin Rivers

Tompolo ya bayyana cewa yana da kyakkyawar alaka da tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, wanda a yanzu ke rike da mukamin Ministan Babban Birnin Tarayya.

Duk da haka, Tompolo wanda ya cika shekaru 54 ya tabbatar da cewa hakan ba ya nufin yana goyon bayan cin zarafin al’ummar Ijaw ba ne.

Kara karanta wannan

"Mutum 1 ke juya APC," Tsohon mataimakin shugaban PDP ya faɗi shirin da suke yi

Punch ta wallafa cewa jagoran Ijaw ya ce:

“Mutane na cewa na ci amanar Ijaw saboda ban yi magana ba game da dakatar da Gwamna Fubara, ku sani ba zan taba cin amanar jama’ata ba.
"Rayuwata gaba ɗaya sadaukarwa ce ga Ijaw.”

Ya ce ana gudanar da tattaunawa tsakanin Wike da Fubara domin shawo kan sabanin da ke tsakaninsu, tare da kwantar da hankalin jama’ar Jihar Rivers da cewa abubuwa za su daidaita.

Fubara
Tompolo ya ce yana kokarin sasanta Wike da Fubara. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Nyesom Ezonwo Wike
Asali: Facebook

Tompolo ya bukaci Ijawa su rungumi juna

A cewar Tompolo, lokaci ya wuce na maida hankali kan maganganun da ke kokarin raba kan Ijawa, yana mai cewa:

“Al’ummar Ijaw ta waye, kuma ba za ta bari a mayar da ita baya ba.”

Ya kuma jaddada bukatar hada kai tsakanin kabilun Ijaw da Itsekiri, yana mai cewa INEC ta bayyana gaskiya kan rade radin a raba mazabun yankin.

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

Tompolo ya ce duk wanda ya yi yunkurin tayar da rigima a Bayelsa zai gamu da martani mai zafi, yana mai cewa lokaci ya yi da Ijaw za su kare junansu.

Kantoman jihar Rivers ya yi nade nade

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban rikon Rivers ya nada mukamai tare da yin kwaskwarima ga wasu hukumomi.

Shugaban rikon ya nada shugabannin kananan hukumomi da za su taimaka masa wajen jagorantar jihar na rikon kwarya.

An fara korafi kan matakin da shugaban rikon ya dauka kasancewar wata kotu ta hana shi yin nade nade tana mai cewa ba shi da hurumin hakan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng