2027: Gwamnan APC Ya Fadi Matsayar Jam'iyyar kan Hadakar 'Yan Adawa

2027: Gwamnan APC Ya Fadi Matsayar Jam'iyyar kan Hadakar 'Yan Adawa

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya taɓo batun yunƙurin da ƴan adawa ke yi na yin haɗaka domin tunkarar zaɓen 2027
  • Uzodimma wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, ya ce ko kaɗan jam'iyyar ba ta damu da yunƙurin yin haɗaka da ake yi ba
  • Gwamnan ya nuna cewa jam'iyyar APC na da ƙarfi kuma ta san hanyoyin yin nasara a zaɓe domin ta saba samun nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, ya yi magana kan yunƙurin da ƴan adawa ke yi na yin haɗaka domin kayar da Shugaba Bola Tinubu.

Gwamna Uzodimma ya bayyana cewa yunƙurin yin haɗakar bai da amfani, inda ya ce jam'iyyar APC ba ta damu da hakan ba ko kadan.

Hope Uzodimma
Gwamna Uzodimma ya ce APC ba ta damu da batun hadaka ba Hoto: Hope Uzodimma
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da wasu manema labarai a Legas.

Kara karanta wannan

Duk da ikon da APC da shi a jihohi 21, Ganduje ya fadi shirin kwato ƙarin wasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnan APC ya ce kan haɗaka?

Gwamna Uzodimma wanda shi ne Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC ya ce ƴan Najeriya ne za su yanke hukunci kan makomar APC a zaɓen 2027.

"Me ake nufi da haɗaka? Muna aiwatar da dimokuraɗiyyar jam’iyyu ne, ba dimokuraɗiyyar haɗaka ba."
"Dimokuraɗiyyar jam’iyyu na nufin shiga jam’iyya don tsayawa takara. Idan jam’iyyarka ta rasa tasiri kuma kana neman hanyar farfadowa, dole ne ka farfaɗo daga suma kafin ka fara tunanin yin haɗaka."
“Ina so na fara da cewa ba a canza tawagar da ke cin nasara. Mun san inda muka fito, inda muke yanzu, da kuma inda muka nufa."
"A ƙarshe dai, ƴan Najeriya ne za su yanke mana hukunci, amma har yanzu akwai lokaci mai yawa kafin hakan. Gwamnatimmu tana da fiye da shekaru biyu a gaban ta kafin wa’adin ya ƙare."

-Gwamna Hope Uzodimma

Hope Uzodimma
Hope Uzodimma ya yi magana kan hadakar 'yan adawa Hoto: Hope Uzodimma
Asali: Facebook
“Idan ka mai da hankali kan cin zaɓe na gaba, alhali ƴan kasa sun ba ka amanar shekaru huɗu, amma baka ma cika biyu ba, hakan ya zama karkatar da hankali."

Kara karanta wannan

Babban kusa a APC ya ba 'yan adawa sirrin kayar da Tinubu a 2027

"Wannan gwamnati ba ta kauce daga abinda ya kawo ta ba. APC a ankare take, kuma ba za mu bar kowa ya ƙwace mana mulki ba. Ba bacci muke yi ba."
“APC ita ce jam’iyya mai mulki, kuma ba a sauya ƴan wasa da ke cin nasara. Idan ɗan wasa na nasara, sai ka ci gaba da saka shi. A ganina, APC jam’iyya ce mai ƙarfi, kuma muna da niyyar ci gaba da gina kasa."

- Gwamna Hope Uzodimma

Ganduje ya yi wa ƴan adawa raddi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi martani ga ƴan adawa kan shirinsu na yin haɗaka.

Ganduje ya bayyana cewa yunƙurin da ƴan adawan ke yi na haɗaka ba abu ba ne wanda zai yi nasara.

Shugaban na APC ya bayyana cewa ko kaɗan jam'iyyar ba ta damu da yunƙurin ba, domin ta san ba zai kai ga ci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel