Babban Kusa a APC Ya ba 'Yan Adawa Sirrin Kayar da Tinubu a 2027

Babban Kusa a APC Ya ba 'Yan Adawa Sirrin Kayar da Tinubu a 2027

  • Ƙusa a APC a Najeriya, Abayomi Mumuni, ya bayyana cewa jam'iyyun adawa sun baro shiri tun rani kan kayar da Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Jigon na APC ya bayyana cewa babu wata jam'iyyar da za ta kayar da Shugaba Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027
  • Abayomi Mumuni ya nuna cewa ƴan adawan ba su da haɗin kai sannan ba su da manufofin da za su jawo hankalin ƴan Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani babban jigo a jam’iyyar APC, Abayomi Mumuni, ya yi magana kan shirin jam'iyyun adawa dangane da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Abayomi Mumuni ya bayyana cewa babu wata jam’iyyar adawa a halin yanzu da ke da cikakken tsarin da za ta iya kayar da Shugaba Bola Tinubu.

Bola Ahmed Tinubu
Jigo a APC ya ce 'yan adawa ba za su iya kayar da Tinubu ba a zaben 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Abayomi Mumuni ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin yaɗa labarai, Rasheed Abubakar, ya rabawa manema labarai, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya yi fallasa, ya fadi korafin jiga jigan APC kan Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigo a APC ya faɗi kuskuren ƴan adawa

Yayin da yake magana, Abayomi Mumuni ya ce duk da cewa tsarin siyasa a Najeriya yana da sarƙaƙiya, amma a bayyane yake cewa mafi yawan jam’iyyun adawa ba su da isasshen haɗin kai don yin takarar shugaban ƙasa a 2027.

Ya ƙara da cewa rashin haɗin kai da rashin bayyana manufofin da za su ja hankalin masu kaɗa ƙuri’a suna daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.

“Yayin da muke duba yadda siyasa take tafiya a halin yanzu a Najeriya, wajibi ne mu yi nazari game da irin ƙarfin da muke da shi da kuma yadda za mu tsara hanyoyin da za su kai mu ga nasara a zaɓen 2027."
"Gaskiyar ita ce, a wannan lokaci, babu wata jam’iyyar adawa da ke da sahihin tsari da za ta iya ƙalubalantar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu."
“Tsarin siyasa a Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba. Amma a bayyane yake cewa jam’iyyun adawa da dama na fama da rashin haɗin kai da zai basu damar tsayawa takarar shugabancin ƙasa."

Kara karanta wannan

"Akwai damuwa," Sanata Ndume ya yi magana kan haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027

"Rashin dunƙulewa waje ɗaya da kuma rashin manufofin da za su ja hankalin jama’a, babbar matsala ce."
“Idan aka duba tarihi, nasarar jam’iyyun adawa ta fi samuwa ne a lokacin da suka samar da tsari mai ƙarfi tare da manufofi masu kyau da suka yi daidai da buƙatun jama'a."
"A halin yanzu, jam’iyyun adawa sun kasa samun haɗin kai a tsakaninsu, wanda hakan ya da sa ayar tambaya kan ko za su iya ƙalubalantar jam'iyya mulki da gaske a 2027."

- Abayomi Mumuni

Sanata Ali Ndume ya soki Bola Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya soki salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Ali Ndume ya bayyana shugaban ƙasan Bola Tinubu ya mayar da jiga-jigan jam'iyyar APC saniyar ware a gwamnatinsa.

Ndume ya bayyana cewa shugaban ƙasan bai bari waɗanda suka wahalta masa, su samu damar ganinsa domin su tattauna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng