Nada Sabon Limamin Abuja Ya Sanya Tinubu Samun Goyon Baya a Zaben 2027

Nada Sabon Limamin Abuja Ya Sanya Tinubu Samun Goyon Baya a Zaben 2027

  • Wata ƙungiyar dattawa a yankin Kudu Maso Gabas ta nuna goyon bayanta ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
  • Ƙungiyar ta ce yankin ya ci gajiyar mukamai ciki har da samun limamin babban masallacin Abuja na farko dan kabilar Ibo
  • 'Yan kungiyar sun roƙi Tinubu ya kawo kudurin ƙirƙirar sababbin jihohi tare da sauƙaƙa matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu- Wata ƙungiyar siyasa a Enugu ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takara a zaben 2027.

Batun yanke matasayar ya fito ne daga wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar suka fitar bayan kaddamar da reshen ƙungiyar a garin Nsukka, Jihar Enugu.

Tinubu
Dattawan Kudu maso Kudu sun goyi bayan Tinubu a 2027. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa sanarwar ta nuna cewa yankin Kudu Maso Gabas ya ci moriyar mulkin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwato manyan bindigogi, sun gwabza fada da 'yan fashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin waɗanda suka sa hannu a sanarwar har da shugaban kungiyar Hon. Humphrey Nsofor, Farfesa Damian Opata, Farfesa Chuka Ezema da Dr. Anthony Alumona.

Batun nada limamin Abuja da wasu mukamai

A cewar ƙungiyar, daga cikin gagarumin ci gaban da yankin ya samu akwai nadin Farfesa Iliyasu Usman a matsayin dan kabilar Ibo na farko da ya zamo limamin Abuja.

Kungiyar ta kara da cewa Bola Tinubu ya nada Emmanuel Ikechukwu Ogalla dan yankin Nsukka a matsayin shugaban rundunar sojin ruwan Najeriya.

Haka zalika ta ce an kara wa Frank Mba matsayi zuwa DIG na ‘yan sanda, sai kuma Farfesa Melvin Ayogu da aka naɗa a kwamitin hukumar CBN.

Yan kabilar Ibo
Dattawan Kudu maso Kudu sun yaba wa Tinubu game da ba su mukamai. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Cikin mutanen da suka samu mukamai a yankin akwai Dr Amaka Onu, Hon. Favour Asogwa da Eva Asadu da suka samu mukamai daban daban.

A karkashin haka suka ce sun ci moriyar gwamnatin Bola Tinubu kuma saboda haka suke goyon bayan shi a zaben 2027.

Kara karanta wannan

2027: Kungiyoyin Arewa 65,000 sun bayyana matsayarsu kan takarar Tinubu

Bukatar rage tsadar rayuwa da kirkirar jihohi

Dattawan sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gabatar da kudurin doka zuwa majalisar tarayya domin ƙirƙirar sababbin jihohi a ƙasar.

Sun ce hakan zai ba shi damar kafa tarihi a matsayin shugaban farar hula na farko da ya ƙara jihohi.

Haka kuma, sun buƙace shi da ya sauƙaƙa matsanancin yanayin tattalin arziki da kuma karya farashin kayan masarufi.

Sun ce dawo da tallafi da daidaita canjin Naira zai taimaka matuƙa wajen rage radadin rayuwa da ake fama da shi.

Kungiyar ta roƙi ‘yan Najeriya su marawa Shugaba Tinubu baya domin kammala mulkin shekara takwas a kudancin Najeriya.

Bola Tinubu zai kawo tallafin kasuwanci

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta kawo shirin tallafin kasuwanci na Naira biliyan 300 domin saukaka wa matasa harkokin rayuwa.

Ministan ilimi ne ya bayyana shirin gwamnatin inda ya ce duk wanda ya gama makaranta kuma ya cancanta, zai iya samun tallafin N10m zuwa sama.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an kawo shirin ne domin ba matasa damar dogaro da kai da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel