"Na Yi wa Allah Alƙawari," Gwamna Alia Ya Yi Magana da Aka Fara Raɗe Raɗin Zai Bar APC
- Mai girma Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa yana shirin tattara kayansa ya bar jam'iyyar APC
- Rabaran Alia ya ce yana nan daram a APC sai ya cika alkawarin da ya ɗaukar wa Allah, kansa da al'umma na ceto Benuwai daga taɓarbarewa
- Gwamnan ya kuma musanta cewa alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da sakataren gwamnatin tarayyya, George Akume, ya ce bai san da zancen ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa ba shi da wani shirin barin APC duk da rikicin cikin gida da ke ci gaba da wakana a cikin jam’iyyar.
Jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya na ɗaya daga cikin jihohin da APC ke fama da rikicin shugabanci, inda jam'iyyar ta dare gida biyu.

Kara karanta wannan
"Zan ba gwamna mamaki," Sanata Nwoko ya yi ƙarin haske kan jihar da ake shirin ƙirƙirowa

Asali: Facebook
Gwamna Alia ya ce yana nan daram a APC yayin wata hira da manema labarai a gidan gwamnati da ke Makurdi, babban birnin jihar, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Alia zai fice daga jam'iyyar APC?
“Ina nan, ba zan je ko ina ba,” in ji gwamnan, yana mai zargin masu yada jita-jitar barinsa jam’iyyar da neman tayar da zaune tsaye a jihar.
Gwamna Alia ya ce ya na da alkawari tsakaninsa da Allah da kansa da kuma jama’ar Benue, wanda hakan ne ya sa ya bar aikinsa na limamin cocin Katolika bayan shekara 35 domin ceton jihar daga halin tabarbarewa.
“Ina da alhakin cika alkawari da na dauka kafin na hau kan wannan kujera. Na zo siyasa ne don in gyara jihar Benue da dawo da martabarta,” in ji shi.
Gwamnatin Benuwai na gina manyan tituna
Ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiwatar da manyan ayyuka kamar gina tituna masu tsawon fiye da kilomita 300, biyan albashi da fansho, da tallafawa manoma da kayayyakin noma da tabbatar da tsaro.
“Akwai wasu da suke jin haushi saboda sun saba da cin gajiyar arzikin jihar su kadai, amma ni ina aiki domin daukacin al’umma ba wani tsirarun mutane ba,” in ji Alia.

Asali: Facebook
Alaƙa ta yi tsami tsakanin gwamna da Akume?
Game da rade-radin sabani tsakaninsa da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, Gwamna Alia ya ce babu wata matsala tsakaninsu.
“Akume jagorona ne, kuma ina girmama shi. Idan akwai wani sabani, ni ban sani ba.”
A karshe, gwamnan ya tabbatar da cewa zai ci gaba da hada kan mambobin jam’iyyar APC a jihar tare da tabbatar da cewa kowanne dan kasa na amfana da romon dimokuradiyya.
Wani ɗan APC a Kaduna, Aliyu Zaharadden ya shaidawa Legit Hausa cewa ba ya tunanin wani gwamna zai bar jam'iyya mai mulki zuwa tsagin adawa.
Amma a cewarsa, daga nan zuwa zaɓen 2027, yana da yaƙinin wasu gwamnonin adawa za su shigo APC.

Kara karanta wannan
Mai magana da yawun PDP ya yi murabus daga muƙaminsa, ya tona asirin wasu shugabanni
"Abubuwan da ke faruwa Benue ba su mana daɗi amma kamar yadda gwamna ya faɗa, babu wani saɓani tsakaninsa da Akume, ina da yaƙinin APC karkashin Ganduje za ta warware komai.
"Za ka ce na faɗa mana, kafin zaɓen 2027 za a samu gwamnonin da za su dawo APC amma ba dai wani ya fita ba, ba za mu bar haka ta faru ba in Sha Allah," in ji shi.
Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari
A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar APC sun ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna.
Shugaban kungiyar Gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma ne ya jagoranci tawagar zuwa gaishe da Buhari.
Uzodinma ya ce sun je ne don nuna girmamawa da fatan alheri ga Buhari, tare da taya shi murnar kammala azumi lafiya da komawa Kaduna da zama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng