Tsohon Ɗan Majalisa Ya Hango Wanda Zai Ci Zaɓe idan Atiku, Obi da El Rufai Suka Haɗe a 2027

Tsohon Ɗan Majalisa Ya Hango Wanda Zai Ci Zaɓe idan Atiku, Obi da El Rufai Suka Haɗe a 2027

  • Tsohon dan majalisar dokokin jihar Lagos, Olusola Sokunle, ya ce babu wata hadaka da za ta zama barazana ga Bola Tinubu a zabe
  • Ya bayyana cewa Tinubu ya fi wadanda ke hada hadakar siyasa, saboda haka suna bata lokacinsu ne kawai, amma ba za su yi tasiri ba
  • Sokunle ya kara da cewa ayyukan Tinubu a kasar nan sun jawo masa soyayyar 'yan Najeriya, don haka ba su jin ko dar a zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaTsohon dan majalisar dokokin jihar Lagos, Olusola Sokunle ya ce babu wata hadaka da da za ta kawo cikas ga nasarar Bola Tinubu a shekarar 2027 idan zai sake neman takara.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi da El Rufai na shirin haɗewa, Tinubu ya bude kofar kayar da shi a 2027

Sokunle, wanda ya wakilci mazabar Oshodi-Isolo I daga shekarar 2015 zuwa 2023 a Majalisar Dokokin Jihar Lagos, ya ce Tinubu ba zai fuskanci wata babbar barazana ba wajen sake cin zabe ba.

Atiku
Ana ganin hadakar su Atiku ba za ta yi tasiri a 2027 ba Hoto: Mr. Peter Obi/Bayo Onanuga/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa dan majalisar ya mayar da martani ne kan batun hadakar wasu jam'iyyun kasar nan, a kokarinsu na sake tabbatar da Tinubu ya fadi zabe mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: An yi watsi da hadakar su Atiku

Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa hadakar su Atiku Abubakar ba za ta yi tasirin komai wajen kawo cikas ga APC a zabe mai zuwa ba.

Ya ce:

“Mun ji batun kafa hadakar wasu shugabannin adawa a cikin PDP da LP domin kalubalantar sake zaben Shugaba Bola Tinubu, kuma na yi dariya saboda na san da tabbas cewa Tinubu zai ci zaben cikin sauki.”
Atiku
Atiku, El Rufa'i da Obi sun shirya kawancen jam'iyyu Hoto: Mr. Peter Obi/Atiku Abubakar/Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

“Ina tabbatar da cewa babu wata hadaka da za ta iya aiki a kan Shugaban kasa; yana aiki da kyau kuma 'yan Najeriya za su sake zaben shi. Haka kuma, wannan hadakar ba za ta yi nasara ba saboda Shugaba Tinubu yana fahimci wasan fiye da wadanda ke hada kai a wannan hadakar.”

Kara karanta wannan

"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi

Sola Sokunle yabi kwarewar Bola Tinubu

Olusola Sokunle ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa kokarinsa na gyara kasar, yana mai cewa'yan kasar nan suna ganin kokarin da ya ke yi..

Ya ce:

“Shi mutum ne mai kwarewa; kwararren mai tsara abubuwa ne. Wadanda suke cikin wannan hadakar su daina bata lokacinsu."

Sokunle ya ce aikin Shugaba Tinubu tun daga lokacin da ya hau mulki a 2023, ya jawo masa samun goyon bayan ‘yan Najeriya da yawa.

Tsohon dan majalisar ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu kan dukkan matakan da ya dauka na inganta tattalin arzikin kasa, da tabbatar da tsaro da jin dadin al’umma.

Ana hasashen Tinubu zai fadi zaben 2027

A baya, mun ruwaito cewa jagoran a SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu ya bude kofar da za a kayar da shi a babban zaben 2027 da kowa ke hari.

Kara karanta wannan

'Arewa ta hada kai da Kudu maso Gabas': An ji dabarar kwace mulki daga hannun Tinubu

Adebayo, wanda ya taba tsayawa takarar shugaban kasa, ya bayyana cewa a halin yanzu, Tinubu yana daukar matakai da za su jawo faduwar jam'iyyarsa ta APC cikin sauki.

A cikin wata tattaunawa da ya yi, Prince Adebayo ya bayyana cewa, a ganin sa, yana da tabbacin cewa jam'iyyar SDP za ta iya kayar da Tinubu da APC a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng