Mai Magana da Yawun PDP Ya Yi Murabus daga Muƙaminsa, Ya Tona Asirin Wasu Shugabanni
- Mai magana da yawun jam'iyyar PDP a jihar Ondo, Kennedy Peretei ya yi murabus daga muƙaminsa, sannan kuma ya fice daga jam'iyyar gaba ɗaya
- A wata wasiƙa da ya aike wa shugaban PDP na gundumarsa, jigon ya zargi shugabanni da maida jam'iyyar hanyar kasuwancinsu a zaɓe
- Ya ce ya jima yana yi wa PDP hidima amma ba zai iya ci gaba da zama a wurin da babu tunanin samar da ci gaba da makoma mai kyau ga al'umma ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Skaataren Yaɗa Labarai na Jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo, Kennedy Peretei, ya ajiye mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar.
Tsohon mai magana da yawun PDP ya caccaki shugabannin jam’iyyar da rashin cancanta da gazawar wajen jagoranci yadda ya kamata.

Kara karanta wannan
"Ya ɗauka ni ne," Abin da ya faru da ɗiyar Buba Galadima ta kira Tinubu a wayar salula

Asali: Facebook
Mista Peretei ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Arogbo Ward 1 da ke ƙaramar hukumar Ese-Odo, rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kakakin PDP ya soki shugabanni
A wasiƙar, ya bayyana cewa shugabanni da wasu jiga-jigan PDP a jihar Ondo ba su da niyya ko shirin lashe kowanne irin zaɓe.
A cewarsa, jam’iyyar ta zama wata hanyar cin moriyar siyasa, inda wasu ‘yan tsiraru ke amfani da ita domin biyan bukatunsu na kashin kai a duk lokacin zaɓe.
A ruwayar jaridar Leadership, Peretei ya ce:
“Na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP saboda ba na ganin makoma mai kyau a karkashin shugabancin da ke rike da jam’iyyar a yanzu.
"Sun fi damuwa da amfani da jam’iyyar wajen hada-hadar siyasa fiye da damuwa da ci gaban jama’a ko nasarar jam’iyyar a zaɓe.”
Me yasa kakakin PDP a Ondo ya yi murabus?
Peretei ya ƙara da cewa ya yi hidima sosai ga jam’iyyar, inda ya fara zama sakataren kuɗi daga shekarar 1999 zuwa 2003, sannan daga 2020 zuwa yanzu yana matsayin sakataren yaɗa labarai na jihar.
Duk da wannan sadaukarwa, ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu da suka yi wa jam’iyyar katanga suka mamaye shugabanci ba tare da an ba sababbin jini dama ba.

Asali: Twitter
Ya ce PDP a jihar Ondo tana cikin mawuyacin hali, ya bayyana cewa jam’iyyar “ta bar dakin kulawaa yanzu tana kan hanyar zuwa dakin ajiye gawawwaki.”
A ƙarshe, Mista Peretei ya shawarci mambobin jam’iyyar da suka dogara da kuɗin zaɓe da tallafi na jam’iyya su nemi wata sahihiyar hanyar rayuwa, maimakon zama 'yan amshin shata ko almajirai na siyasa.
Ɗan Majalisa ya fice daga LP zuwa PDP
A wani rahoton, kun ji cewa mamba mai wakiltar mazaɓar Isi-Uzo a majalisar dokokin jihar Enugu, Eze Gabriel, ya sauya sheka daga jam'iyyar LP zuwa PDP.
Hon. Eze ya sanar da matakin da ya ɗauka ne a wata wasika da ya miƙa wa Majalisar dokokin a zaman ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, 2025.
Ɗan Majalisar ya bayyana damuwa cewa ba a son ransa ya ɗauki matakin barin LP ba sai don ya zama dole.
Asali: Legit.ng