Rivers: Gwamnoni 11 a Najeriya Sun Maka Tinubu a gaban Kotun Koli game da Fubara
- Gwamnonin jam’iyyar PDP guda 11 sun shigar da kara a kotun koli don kalubalantar dokar ta-baci da aka kafa a jihar Rivers
- Gwamnonin daga Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara da Bayelsa ne suka shigar da karar
- Sun kalubalanci dakatar da Gwamna Simi Fubara da mataimakinsa, tare da nada tsohon hafsan ruwa, Ibok-Ete Ibas, a matsayin shugaban riko
- Gwamnonin PDP na neman kotun koli ta bayyana cewa matakan da Bola Tinubu ya dauka na keta kundin tsarin mulki ne kuma ba bisa ka’ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Gwamnonin jam’iyyar PDP sun shigar da kara a gaban kotun koli don kalubalantar kafa dokar ta-baci a jihar Rivers.
An shigar da karar mai lamba SC/CV/329/2025 daga gwamnonin Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara da Bayelsa.

Asali: Twitter
Duk da cewa an sanya ranar 20 ga Maris a takardar kara, an shigar da ita a gaban kotun koli ranar 8 ga Afrilu, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a Rivers
Hakan ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers ranar 18 ga Maris, sakamakon rikicin siyasa.
Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu da dukkan ‘yan majalisar dokoki na jihar har na tsawon wata shida.
Shugaban ya nada tsohon hafsan ruwa mai ritaya, Ibok-Ete Ibas, a matsayin shugaban soja daya tilo da zai kula da jihar.
Majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da bukatar Tinubu na kafa dokar ta-baci duk da cece-kuce daga wasu bangarori.

Asali: Twitter
Musabbabin gwamnonin PDP shigar da Tinubu kara
Gwamnonin PDP na kalubalantar sahihancin matakin Tinubu, musamman ko shugaban kasa na da ikon dakatar da gwamna da mataimakinsa.

Kara karanta wannan
"Ka yi hattara da El-Rufa'i,' Jagora a APC ya shawarci Atiku kan takarar shugaban kasa
Suna kalubalantar dakatar da majalisar dokokin jihar Rivers da kuma nadin shugaban riko daya tilo don jagorantar jihar.
Sun ce matakan da Shugaba Tinubu ya dauka sun ci karo da wasu sashe na kundin tsarin mulki na 1999 na Najeriya, Channels TV ta ruwaito.
Gwamnonin suna bukatar kotun koli ta fayyace ko Shugaban kasa na da ikon sauke gwamna da mataimakinsa da nada nasa wakili.
Suna kuma neman kotun koli ta bayyana dakatar da Fubara da Odu da majalisa da kuma nadin Ibas a matsayin rashin bin doka.
Shugaban riko a Rivers ya yi nade-nade
Kun ji cewa Shugaban riko a jihar Rivers, Ibok-Ete Ekwe Ibas, ya naɗa shugabannin riko na kananan hukumomi 23 na jihar duk da kotu ta hana.
Hakan na zuwa ne bayan wata kotu a Port Harcourt ta hana Ibas ɗaukar irin wannan mataki, tana mai cewa ba shi da hurumin yin nadin bisa dokar kasa.
Wasu na ganin matakin da Ibas ya dauka zai iya kara hura wutar rikici a cikin rikicin siyasa da shari’a da ke ci gaba da kara zafi tun bayan kafa dokar ta-ɓaci a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng