Bayan Wike Ya Gana da 'Yan Majalisa, An Bijirewa Kotu, An Yi Nadin Mukamai a Rivers

Bayan Wike Ya Gana da 'Yan Majalisa, An Bijirewa Kotu, An Yi Nadin Mukamai a Rivers

  • Shugaban riko a Rivers, Ibok-Ete Ekwe Ibas, ya naɗa shugabannin riko a kananan hukumomi 23 na jihar duk da kotu ta hana
  • Wata kotu a Fatakwal ta hana Ibas ɗaukar irin wannan mataki, tana mai cewa ba shi da hurumin yin nadin bisa dokar kasa
  • Ana ganin matakin da Ibas ya dauka zai iya kara hura wutar rikici a cikin rikicin siyasa da shari’a da ke ci gaba da kara zafi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Shugaban riƙon Rivers, Ibok-Ete Ekwe Ibas, ya amince da naɗa shugabannin riko a kananan hukumomi 23 na jihar.

Baya ga haka, an ruwaito cewa Ibok-Ete Ekwe Ibas ya dawo da wasu hukumomi da kwamitocin gwamnati da aka dakatar a baya.

Ibas na Rivers
Shugaban riko na Rivers ya yi nade nade. Hoto: Imrana Muhammad
Asali: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa sanarwar fito ne daga sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibibia Worika, a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ana rade radin Tinubu ya tsige shi, Mahmud Yakubu ya saka labule da ma'aikatan INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubale na siyasa da na shari’a a jihar, musamman bisa hukuncin kotu da ya haramta Ibas ɗaukar irin wannan matakin.

Matakin da kotu ta dauka a jihar Rivers

Kotun Tarayya da ke Fatakwal, a ƙarƙashin Mai Shari’a Adamu Turaki Mohammed, ta bayar da umarnin dakatar da Ibas daga nada shugabannin riko a kananan hukumomi.

Kotun ta amince da roƙon gaggawa da aka gabatar a ranar 28 ga Maris, inda ta hana Ibas ko wakilansa nade nade, tare da sanya ranar 14 ga Afrilu domin sauraron cikakkiyar karar.

Punch ta wallafa cewa duk da umarnin, gwamnatin rikon kwarya ta ci gaba da naɗin shugabanni, wanda hakan ke ƙara tayar da kura a siyasar jihar.

Rikicin kananan hukumomi a jihar Rivers

Rikicin siyasar Rivers ya samo asali tun bayan karewar wa’adin shugabannin kananan hukumomi da aka zaɓa a lokacin tsohon Gwamna Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya fadi hanyar kawo karshen kisan gilla a jihar Filato

Duk da karewar wa’adinsu a watan Yuni 2023, wasu ‘yan majalisa 27 da ke biyayya ga Wike sun yi ƙoƙarin tsawaita wa’adinsu.

Gwamna Siminalayi Fubara, wanda ya gaji Wike, ya rusa shugabancin kananan hukumomin tare da naɗa shugabannin riko, abin da ya jawo wata sabuwar takaddama a jihar.

Halin da ake ciki a siyasar jihar Rivers

Bayan rikici ya yi kamari a Rivers, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar a ranar 18 ga Maris, domin dawo da doka da oda.

Sai dai bayan wannan mataki, rikicin bai lafa ba, domin bangaren Fubara za su iya zargin Ibas da kokarin kauce wa doka ta hanyar nada shugabanni ba tare da izini ba.

Yayin da shari’a ke ci gaba da gudana da kuma sababbin nade nade da aka yi, ana sa ran rikicin siyasar Rivers zai ci gaba da daukar sabon salo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'a a Kebbi cikin dare

Fubara
Gwamnan Rivers da aka dakatar a watan da ya wuce. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Wike ya gana da 'yan majalisar Rivers

A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya gana da 'yan majalisar jihar Rivers da aka dakatar a London.

Lamarin ya dauki hankalin jama'a ganin cewa rikicin majalisar na cikin dalilan da suka janyo saka dokar ta baci a jihar.

Sai dai 'yan majalisar sun bayyana cewa sun tafi London ne domin samun horo na musamman a kan gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng