Nada Mukamai: Sanata Ndume Ya Dura kan Tinubu, Ya ce Bai Tsoron me zai Biyo Baya

Nada Mukamai: Sanata Ndume Ya Dura kan Tinubu, Ya ce Bai Tsoron me zai Biyo Baya

  • Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa nadin mukamai da Shugaba Bola Tinubu ke yi ya saba wa tsarin raba madafun iko da kundin tsarin mulki ya tanada
  • Ya ce rabon mukaman siyasa da aka yi bai nuna daidaito da wakilci daga yankunan ƙasa kamar yadda sashi na 14 (3) na kundin tsarin mulki ke bukata ba
  • Ndume ya ce ba wai yana sukar Tinubu ba ne don son zuciya, amma ya kira hankalin shugaban ƙasa ne domin a gyara abin kafin ya haifar da matsala

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume da ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya soki nadin mukamai da Shugaba Bola Tinubu ke yi.

Sanatan ya yi sukar ne yana mai cewa hakan ya ci karo da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Makomar siyasar Saraki a Najeriya da jita jitar komawa jam'iyyar APC ko SDP

Ndume
Sanata Ndume ya ce Tinubu ya kauce hanya wajen nada mukamai. Hoto: Bayo Onanuga|Senator Ali Muhammad Ndume
Asali: Facebook

Sanata Ali Ndume ya soki nadin mukamai

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise, Ndume ya bayyana cewa yadda ake raba mukaman siyasa yanzu haka bai cika tanadin sashi na 14 (3) na tsarin mulkin 1999 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa tsarin mulkin Najeriya na 1999 na bukatar a bai wa kowane yanki wakilci cikin gwamnati.

Sanata Ndume ya cea:

"Ba wai kawai ina zargin gwamnati ba ne, na nuna alkaluma da suka tabbatar da irin yadda aka saba da tsarin mulki.
"Kuma ba wai ina cewa shugaban ƙasa bai da ikon yin nade-nadensa ba ne, amma dole ne ya bi doka."

Ndume ya bukaci Tinubu ya gyara tafiyarsa

Ndume ya ce dole ne a dinga duba nade-naden da idon doka, domin idan aka ci gaba da yin watsi da tsarin da kundin tsarin mulki ya shimfida, hakan na iya haifar da matsala a gaba.

Kara karanta wannan

'Ka da ka jawo mana rigimar addini': 'Yan sanda ga malamin Musulunci a Gombe

The Cable ta wallafa cewa ya kara da cewa:

“Ina kira ne ga shugaban ƙasa ya gyara wannan lamari kafin ya jawo wani rikici ko rashin jituwa a ƙasa.”

A cewarsa, ‘yan majalisa na da hakkin lura da ayyukan shugaban ƙasa da kuma nusar da shi idan an samu karkacewa daga doka, ya ce hakan shi ne manufar kasancewarsu a majalisar dokoki.

Ndume ya ce ba ya jin tsoron komai

Sanatan ya ce bai tsoron suka ko barazana daga magoya bayan Tinubu, yana mai cewa yana magana ne a matsayin ɗan ƙasa wanda kundin tsarin mulki ya ba shi 'yancin bayyana ra’ayinsa.

Ali Ndume ya ce:

"Wasu daga cikin mutanen gwamnati za su fara kai hari a kaina, ba sa duba abin da aka fada sai mai maganar.
"Amma wannan batu ba na Ndume ba ne, batu ne da ya shafi gaskiya da adalci ga Najeriya,”

Kara karanta wannan

Wike ya fadi halin da yake ciki bayan cewa ya yanki jiki ya fadi, an tafi da shi Faransa

Ndume
Ndume ya bukaci Bola Tinubu ya sauya salon nada mukamai. Hoto: Senator Ali Mohammed Ndume
Asali: Twitter

SDP ta ce za ta doke Bola Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar SDP mai alamar doki ta ce ta shirya kayar da shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo ne ya bayyana haka yayin da yake fashin bakin kan lamuran siyasa.

Adebayo ya ce suna kyautata zaton cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi za su shiga tafiyar SDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng